Kasar Jamus Ta Ce Tana Goyon Bayan Yerjejeniyar Nukliya Da Iran
Ministan harkokin wajen kasar Jamus ya kara jaddada cewa gwamnatinsa tana goyon bayan yerjejeniyar Nukliyar da aka cimma tare da Iran duk tare da irin adawar da gwamnatin Amurka take da ita.
Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar China ya nakalto kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Jamus Rainer Breul yana fahar haka, ya kuma kara da cewa kare yerjejeniyar shirin Nukliyar kasar Iran yana daga cikin abubuwan da kasar Jamus take bawa muhimman don ganin zaman lafiya ta wanzu a duniya.
Breul ya ce yerjejeniyar da kasashe 7 da kum kungiyar tarayyar Turai ta amince da ita ba zai yu a sauyata da sauki ba. sai dai kakakin ma'aikatar harkokin wajen na kasar ta Jamus ya ce Jamus ba zata so a sake matanin yerjejeniyar ta yanzu ba, amma tana goyon bayan a nemi hanyar warware matsalolin da suka taso daga baya bayan nan kan shirin makamai masu linzamin kasar Iran.