Sojojin Yemen Sun Tarwatsa Wani Sansanin Sojin Saudiyya A Yankin Asir
(last modified Sun, 06 May 2018 11:19:30 GMT )
May 06, 2018 11:19 UTC
  • Sojojin Yemen Sun Tarwatsa Wani Sansanin Sojin Saudiyya A Yankin Asir

Sojojin Yemen da suke sami dauki dakarun sa kai na kasar sun kai hari kan wani sansanin sojin Saudiyya da yake yankin Asir da makamai masu linzami inda suka tarwatsa wajen.

Tashar talabijin din al- Masirah ta kasar Yemen, cikin wani rahoto da watsa a yau din nan Lahadi, ta bayyana cewar dakarun kasar Yemen din sun harba wasu makamai masu linzami samfurin Zalzal 2 zuwa sansanin soji na Ain al-Thwareen na kasar Saudiyya, a matsayin mayar da martani ga hare-hren da Saudiyya da kawayenta suke ci gaba da kai wa kasar inda suka tarwatsa wajen da kuma haifar da hasarori ga snsanin.  

Haka nan wasu rahotannin ma sun ce sojojin na Yemen sun hallaka wasu sojojin Saudiyya biyu a wani hari da suka kai sansanin sojin Saudiyyan na Haskul da ke yankin Jizan.

Wadannan hare-hare dai suna zuwa ne a matsayin mayar da martani ga hare-haren wuce gona da irin Saudiyyan da kawayen suke kai wa kasar ta Yemen musamman a yankunan Sa'ada, Hudaydah da Hajjah da jiragen yakin Saudiyyan suka yi musu ruwan bamai-bamai.