Kasashe 14 Na Gungun Lima Sun Janye Jakadunsu A Venezuela
Kasashe 14 na gungun Lima sun sanar da kiran jakadunsu a kasar Venezuella, sa'o'i kadan bayan da shugaba Nicolas Maduro, ya sake lashe zaben shugaban kasar.
Kasashen 14 da suka hada da Argentina, Brazil, Kanada, Chili, da Columbia da kuma Mexico, sun ce sun dau matakin ne don mayar da martani kan zaben da suka danganta da marar sahihanci wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa na zabe.
Shi dai bayan ayyana shi a matsayin dan takarar da ya lashe zaben shugabancin kasar ta Venezuala, Mista Maduro ya kirayi dukkanin 'yan adawar kasar musamman wadanda suka yi takara da shi zuwa ga zaman tattaunawa da nufin lalubo hanyoyin warware matsalolin da kasar ta shiga.
A jiya Lahadi ne dai al'ummar kasar ta Venezuella suka kada kuri'a a zaben shugaban kasar, wanda shugaba mai ci Nicolas Maduro ya lashe da kashi 68 cikin dari na yawan kuri'un da aka kada, lamarin da ya bashi nasarar lashe zaben a zagayen farko wanda kuma zai bashi damar ci gaba da shugabancin kasar har zuwa shekara 2025.