Za A Gudanar Da Zabe Cikin Watan Disemba A Libiya
Jagororin Libiya Sun amince a gudanar da zaben kasar a ranar 10 ga watan Disemba a taron zaman lafiyar da suka gudanar yau Talata a birnin Paris na kasar Faransa
Kamfanin dillancin labaran Anatolia ya habarta cewa sakamakon taron zaman lafiya na kasar Libiya da ya gudana a birnin Paris ya amince da gudanar da zaben 'yan Majalisa a ranar 10 ga watan Disemba na karshen wannan shekara ta 2018.
Wannan taro shi ne na farko da ya hada jagororin kasar ta Libiya da suka hada da Janar Khalifa haftar babban hafsan sojojin kasar da Akila Saleh Isa, shugaban majalisar Congres na kasar, da Khalif Almashiry shugaban majalisar Koli na gwamnatin kasar da Faiz Siraj Piraministan kasar ta Libiya wuri guda.
Har ila yau taron ya samu halartar kasashe makobtan Libiya, da kuma wadanda batun ya shafa da aka gayyata a taron wadandan suka hada da Chadi, Nijar, Tunisia, Aljeriya da Masar, sai kuma Congo Brazzaville a daya bangare, dake halartar taron.har ila yau taron ya samu halartar Musa Fakki Muhamad shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka da Gassan Salama manzon musaman na Majalisar Dinkin Duniya.
Kasar Libiya dai ta fada cikin rikici tun bayan kifar da gwamnatin marigayyi kanal Mu'amar Kaddafi a shekarar 2011.