An Saki Yan Adawa A Kasar Venezuela Daga Gidan Kurkuku.
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Madoro ya bada umurnin sakin wasu yan adawa da gwamnatnsa daga gidan yari.
Kamfanin dillancin labaran kasar Fars na kasar Iran ya nakalto Daniel Ceballos shugaban komitin kare kundin tsarin mulkin kasar Venezuela ya na fadar haka a jiya jumma'a. Ya kuma kara da cewa magajin garin yanki San Cristobol na daga cikin yan adawan da shugaban ya bada umurnin a sake su.
Majiyar sharia ta kasar Venezuela ta kara da cewa nan gaba ma ana saran shugaban zai bada umurnin sake karin wasu yan adawan da ake tsare da su.
A makon da ya gaba ne shugaba Nicolas Madoro ya yi rsantsuwar kama aiki karo na biyu, kuma a rannan ma ya bada unurnin a saki wasu yan adawa 4 masu zanga zanga wadanda aka tsare jim kadan kafin zaben.