An Zabi Sabbin Membobin Kwamitin Tsaro Na Wa'adin Shekaru Biyu
Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya zabi kasashen Jamus, Belgium, Afirka ta Kudu, Jamhuriyar Dominica da kuma Indonusiya a matsayin sabbin membobin Kwamitin Tsaro na Majalisar na wa'adin shekaru biyu.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce a kuri'ar da aka kada a jiya Juma'a an zabi kasashen Jamus, Belgium, Afirka ta Kudu da kuma Jamhuriyar Dominica a matsayin membobin kwamitin tsaron kai tsare ba tare da yin takara da wasu kasashe ba, alhali ita kuwa kasar Indonusiya sun yi takara ne da kasar Maldives don samun kujerar da aka ware wa nahiyar Asiya-Pacific inda ta sami kuri'u 144, ita kuma kasar Maldives ta sami kuri'u 46.
Su dai wadannan kasashe biyar din za su maye gurbin kasashen Netherlands, Sweden, Ethiopia, Bolivia da Kazakhstan ne wadanda wa'adin mulkinsu zai kare a karshen shekara inda za su hadu da kasashen Ivory Coast, Equatorial Guinea, Kuwait, Peru da kuma Poland a matsayin membobin kwamitin tsaron wadanda ba su da kujeru na dindindin a Kwamitin tsaron.
Kwamitin tsaron dai wanda shi ne sashin Majalisar Dinkin Duniya da ke da hakkin fitar da kuduri na wajibi a kan kasashe da kuma sanya wa kasashe takunkumi ko ma ba da umurnin amfani da karfi, yana da membobi biyar masu kujera ta dindindin kana kuma masu karfin hawa kujeran naki a kwamitin wadanda su ne Amurka, Rasha, China, Birtaniya da kuma Faransa.