Jun 16, 2018 06:29 UTC
  • Ministan Harkokin Cikin Gidan Jamus Ya Kori Shugabar Majalisar Kula Da 'Yan Gudun Hijirar Kasar

Ministan harkokin cikin gidan kasar Jamus ya tsige shugabar Majalisar Kula da 'yan gudun hijirar kasar daga kan mukaminta.

Kakakin ma'aikatar harkokin cikin gidan gidan kasar Jamus a jiya Juma'a ya sanar da cewa: Ministan harkokin cikin gidan kasar ta Jamus Horst Seehofer ya tsige Madam Utah Kurt shugabar Majalisar kula da 'yan gudun hijirar kasar daga kan mukaminta.

Rahotonni sun bayyana cewa: Tsige Madam Utah Kurt daga kan mukaminta baya rasa nasaba da matakin da ta dauka na amincewa da bukatar 'yan gudun hijira 4,600 ta neman mafaka a kasar ta Jamus.

Ministan harkokin cikin gidan kasar Jamus Horst Seehofer shugaban jam'iyyar CSU da ke mara baya ga jam'iyyar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel yana tsananin adawa da batun karbar 'yan gudun hijira a kasar.  

Tags