MDD Ta Yaba Wa Aljeriya Akan Yaki Da Ta'addanci
(last modified Wed, 27 Jun 2018 07:22:29 GMT )
Jun 27, 2018 07:22 UTC
  • MDD Ta Yaba Wa Aljeriya Akan Yaki Da Ta'addanci

Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya a yammacin Afirka ne ya yi kira ga sauran kasashe da su yi koyi da Aljeriya akan yadda ake fada da ayyukan ta'addanci.

Muhammad Bin Chambas wanda ya gana da ministan harkokin wajen kasar Aljeriya, Abdulkadir Musahil, ya ce taimakon da Aljeriya take yi wa kasashen yammacin Afirka da kuma yankin Sahel a fadan da suke yi da ayyukan ta'addanci wani abu ne da Majalisar Dinkin Duniya take jinjinawa.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a yammacin Afirka ya ce; A wannan lokacin muna fuskantar babbar matsalar tsaro a yammacin Afirka, amma Aljeriya tana nuna mana hanyar fada da wuce gona da iri da kuma ta'addanci.

A nashi gefen ministan harkokin wajen Aljeriya ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta hada kai da Majalisar DInkin Duniyar domin fada da ayyukan ta'adanci.