Al'ummar Yemen Miliyan 18 Ne Ke Fama Da Matsalar Karamcin Abinci
Hukumar kula da abinci ta Majalisar dinkin Duniya FAO ta sanar da cewa yaki ya jefa sama da mutane miliyan 18 cikin matsalar karamcin abinci a kasar Yemen.
Tashar talabijin din Almayadin ta nakalto hukumar kula da abinci na MDD a jiya Litinin na cewa yaran kasar Yemen sun dara sauren kasashe Duniya dake cikin hadarin mutuwa saboda da rashin abinci, kuma a halin da ake ciki abinda ke wakana a kasar ta yemen na rashin abinci, bala'i ne da ba a taba ganin irinsa a tarihi ba.
Rahoto ya ce katse hanyar kai agajin abinci, magani da makamashi da kawancen saudiya ya yi, ya jefa milyoyin al'ummar yemen cikin yinwa da kuma hakan na iya sanya su rasa rayukansu.
Har ila yau rahoton ya ce sama da 'yan kasar Yemen miliyan uku ne da suka hada da mata masu ciki, da kuma shayarwa gami da kananen yara ke bukatar taimakon gaggauwa na abinci.
Sama da shekaru uku kenan da kawancen kasashen Larabawa bisa jagorancin Saudiya suka killace kasar Yemen ta kasa, sama da kuma ta Ruwa, da hakan ya hana saukar jiragen kai agajin gaggauwa shiga kasar.