Mutane 98 Suka Mutu A Girgizar Kasar Indonusiya
Aug 07, 2018 11:17 UTC
Hukumomi a Indonusiya sun ce mutane a kalla 89 ne suak rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasar data auka wa kasar a tsibirin Lombok.
Har yanzu dai ana ci gaba da aikin ceto don zakulo wadanda lamarin ya rusa dasu.
A jiya Litini dai masu aikin ceto, sun ceto mutane sama da 2,000.
Mafi yawan wadanda girgizar kasar ta rusa dasu, 'yan yawan bude ido ne a yankin tsaunuka dake arewacin Lombbok.
Girgizar kasar mai karfin maki 6,9 data auku a jiya Lahadi, ta haddasa barnar dubban gidaje da gadoji, mako guda bayan wata girgizar kasar data kashe mutum 17.
Hukumomi a arewacin lardin na Lombok, inda nan ne cibiyar girgizar kasar, sun ce girgizar kasar ta lalata kusan kashi 80% na yankin.
Tags