Kasa Ta Sake Girgiza A Indonusiya
Kwanaki hudu bayan mummunar girgiza kasa data auka wa tsibirin Lombok, na Indonusiya, wata girgiza kasa mai karfin maki 6,2 ta sake auka wa yankin a yau Alhamis.
Saidai girgizar kasar bata kai karfin wacce ta gudana ba a kwanakin baya, amma ta hadassa rushewar wasu gidaje wadanda waccen girgizar kasar ta raunana karfinsu.
A halin da ake ciki dai sabbin alkalumman da mahukuntan Indonusiyar suka fitar sun nuna cewa mutane 319 ne suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasa data auka wa tsibirin na Lombok a ranar Lahadi data gabata.
Ko baya ga haka akwai mutane 70,000 wadanda suka rasa matsugunnansu, a daidai kuma lokacin da ruwan sha da kuma abinci da magunguna suka fara wuya a yankin.
Wata matsala da ake fuskanta kuma ita ce yadda shiga wasu kauyuka ke wa masu aikin ceto wahala.