Kungiyar Taliban Za Ta Halarcin Zaman Mascow
Ministan harakokin wajen kasar Rasha ya tabbatar da cewa kungiyar Taliban za ta haslarci zaman da za a yi game da rikicin kasar Afganistan a birnin Moscow.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto ministan harakokin wajen Rasha Sergei Lavrov a wannan talata na cewa kungiyar Taliban na da niyar halartar taron da za a gudanar kan kasar Afganistan ranar 4 ga watan Satumba a birnin Moscow.
Kafin hakan dai, jaridar Wall street Journal ta nakalto wata majiya na cewa kungiyar Taliban ta amince da bukatar Rasha na halartar taron sulhu kan kasar Afganistan da za a gudanar kasar ta Rasha.
Zamir Kabulov Manzon musaman na shugaban kasar Rasha kan kasar Afganistan ya sanar da aika sakon gayyata ga kungiyar Taliban kan taron sulhu a birnin na Moscow.
Mista Kabulov ya ce zaman ba zai takaita ba kan yarjejjeniyar tsagaita wuta ba, saidai zaman zai tattauna kan samar da sulhu mai dorewa a tsakanin al'ummar kasar Afganistan.