An Cimma Sabuwar Yarjejjeniyar Tsaro Tsakanin Iran Da Siriya
(last modified Mon, 27 Aug 2018 08:00:44 GMT )
Aug 27, 2018 08:00 UTC
  • An Cimma Sabuwar Yarjejjeniyar Tsaro Tsakanin Iran Da Siriya

Ministocin harakokin tsaron kasashen Siriya da Iran sun sanya hannu kan wata sabuwar yarjejjeniyar tsaro a jiya lahadi.

Kafar watsa labaran ma'aikatar tsaron Iran ta nakalto Ministan tsaron kasar Brigadier Janar Amir Hatami da takwaransa na kasar Siriya Ali Ayub sun sanya hannu kan wata sabuwar yarjejjeniyar tsaro tsakanin kasashen biyu, bayan tattaunawar da suka yi tsakaninsu a jiya Lahadi, kafin hakan dai ministan tsaron kasar ta Iran ya gana da Shagaba Bashar Asad.

Bayan sanya hanu a wannan yarjejjeniya, ministan tsaron Iran din ya ce kasar Siriya na kan gab da fita daga matsalar 'yan ta'adda, inda kuma za ta shiga cikin halin gina kasa.

Ministan ya kara da cewa da taimakon jamhoriyar musulinci ta Iran kasar Siriya ta samu gagarumar nasara a kan 'yan ta'adda.

A nasa bangare, ministan harakokin tsaron Siriya Ali Ayub ya ce ci gaba da aiki tare tsakanin kasar da Iran shi ke tabbatar da muradun al'ummar Siriya kuma ba za taba bayar da dama na ganin an samu matsala tsakanin alakar kasashen biyu ba.

A safiyar jiya Lahadi ne ministan harakokin tsaron Iran tare da tawagarsa suka fara ziyarar kwanaki biyu a Damuscus babban birnin kasar Siriya.