Girgizan Kasa Mai Ma'aunin Richter 6.2 Ta Aukawa Kudancin Kasar Indonasia
(last modified Tue, 28 Aug 2018 19:06:09 GMT )
Aug 28, 2018 19:06 UTC
  • Girgizan Kasa Mai Ma'aunin Richter 6.2 Ta Aukawa Kudancin Kasar Indonasia

Girgizan kasa mai karfin ma'aunin richter 6.2 ta aukawa kudancin kasar Indonasia da misalin karfe 2:08 na rana.

Hukumar Geological Survey ta Amurka (USGS) ta bayyana cewa garin Kupang mai tazarar kilomita 100 daga babban birnin yankin Nusa ta gabas  ne masomin girgizan kasar. Kuma zurfinta ya kai kilomita 10 karkashin kasa. 

Wani mai magana da yawun gwamnatin jihar Kupang Martha Magdalena ya bayyana cewa girgizan kasar tana da karfi sosai, don haka mutane da dama sun firgita sun kuma ruga zuwa waje daga ofisoshinsu. Har yanzun ba'a bayyana yawan asarori na rayuwa ko na dukiyoyi wanda girgizan kasar ta haddasa ba. 

Har'ila yau ba'a bada sanarwan aukuwan tsunami ba sanadiyar girgizan kasar.  A farkon watan Augutan da muke ciki ma girgizan kasa ta aukawa tsibirin Lombok na kasar ta Indonasia wacce ta jawo mutuwar mutane 550.