Indonesia: Girgizar Kasa Ta Yi Sanadiyar Mutuwa Mutane Kimanin 400
Girgizan kasa mai karfin ma'aunin Richter 7.5 ta aukawa garin Sulawesi na bakin teku a kasar Indonasia a jiya Jumma'a wanda ya haddasa igiyar ruwa mai karfi wacce kuma ta fadawa garin ta kuma kashe kimani mutane 400 ya zuwa yanzu.
Tashar talabijin ta Presstv a nan tehran ta bayyana cewa saurin igiyar ruwan wacce ake kira tsunami ta kai kilomita 800 a ko wace sa'a sannan ta na da tsawon mita 6.
Ambaliyar ruwan da tsunamin ta jawo ya rusa gidaje, tituna da gadoji a yankin, banda haka sun jawo katsewar wutan lantarki da kuma wayar tarko a yankin.
Jami'an bada agajin gaggawa sun bayyana cewa mutane 384 ne aka tabbatar da mutuwarsu sannan wasu 540 suka ji rauni a yayinda wasu 29 suka bace.
Shugaban kasar ta Indonasia ya ziyarci wurin don ganewa idanunsa irin halin da mutanen yankin suka shiga ciki. An rufe tashar jiragen sama na yankin a jiya jumma'a sanadiyyar lalacewar da kayakin aiki a wajen suka yi sanadiyar girgizan kasar da Tsunami. Amma ana saran za'a bude shi a yau Asabar don samun damar kai kayakin agji na gaggawa wadanda suka hada da abinci da ruwan sha.