Girgiza Kasa : Indonusiya Ta Nemi Tallafin Kasashen Duniya
(last modified Mon, 01 Oct 2018 05:40:24 GMT )
Oct 01, 2018 05:40 UTC
  • Girgiza Kasa : Indonusiya Ta Nemi Tallafin Kasashen Duniya

Hukumomi a Indonusiya, sun nemi tallafin kasashen duniya domin tunkarar barnar da bala'in tsunami gami da mummunar girgiza kasar data abkawa kasar a ranar Juma'a data gabata, ta haifar.

Wani jami'in gwamnatin kasar mai suna Tom Lembong, ya shaidawa masu aiko da rahotonni cewa, shugaban kasar Joko Widodo, ya basu damar su karbi tallafin gaggawa na kasashen duniya domin shawo kan bala'in.

Alkalumman baya bayan nan dai sun nuna cewa, adadin mutanen da suka mutu a mummunar girgiza kasa gami da bala'in na tsunami ya kai akalla 832, a yayin da wasu sama da 500 ke cikin mawuyacin hali.

A halin da ake ciki dai masu aikin ceto na ci gaba da maida hankali wajen ceto mutanen da gine gine suka rufta akansu.

Mataimakin shugaban kasar ta Indonusiya, ya ce akwai yiwuwar adadin mutanen da suka mutu ya kai dubbai.