Oct 10, 2018 05:43 UTC
  • MDD Ta Bukaci Aljeriya Ta Daina Tiso Keyar Bakin Haure

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Aljeriya data dakatar da korar bakin haure 'yan Afrika zuwa jamhuriyar Nijar.

Wakilin MDD, mai kula da harkokin kare hakkin bil adama na bakin haure ne, Felipe Gonzalez Morales, ya bayyana hakan a yayin wata ziyarar da ya kai Jamhuriya ta Nijar daga ranar 1 zuwa 8 ga watan nan na Oktoban 2018.

Rahoton ya nuna cewa wasu daga bakin hauren dake aiki a Aljeriya ana korarsu ba tare da ma sun tattara kayansu ba, tare da dukkansu, a kuma tiso keyarsu a iyaka da Nijar cikin hamada.

Dama hukumar kula da bakin haure ta MDD, cewa da OIM ta jima tana sukan yadda Aljeriya ke tiso keyar bakin hauren da karfin tsiya, ba tare da sun kimsa ba, alhali dayewa daga cikin bakin hauren nada iyali da kuma 'ya'ya dake karatu a kasar.

Alkalumman da hukumar ta OIM ta fitar sun nuna cewa bakin haure 'yan Afrika 12 000 ne Aljeriya ta tiso keyarsu tun daga farkon wannan shekara ta 2018. 

 

Tags