Ambaliyar Ruwa Da Zaftarewar Kasa Ta Kashe Mutum 22 A Indonusiya
Oct 13, 2018 11:53 UTC
Hukumomi a yankin Sumatra dake yammacin kasar Indonusiya sun sanar da mutuwar mutane 22 biyo bayan ambaliyar ruwa da zaftarewar data biyo bayan ruwan sama da aka samu tamakar da bakin kwarya a yankin da yammacin jiya Juma'a.
Daga cikin wadanda suka mutun akwai dalibai na wata makarantar kwana ta Islamiya a wani kauye na lardin Mandailing Natal.
Ko baya ga wadanda suka rasa ransu akwai mutane da dama da suka bata a cewar hukumomin yankin.
Bayanan sun ce akwai gidaje da dama da suka lalace bayan wannan iftila'in.
Masu aikin ceto dai na fuskantar kalubale wajen isa a yankunan da iftila'in ya shafa saboda zaftarewar kasa a cewar shugaban hukumar agajin gaggawa na yankin.
Tags