MDD Ta Bukaci Kara Wa'adin Raba Kayayyakin Jin Kai A Siriya
(last modified Tue, 30 Oct 2018 06:17:24 GMT )
Oct 30, 2018 06:17 UTC
  • MDD Ta Bukaci Kara Wa'adin Raba Kayayyakin Jin Kai A Siriya

Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin raba kayayyakin jin kai a Siriya ya bukaci kara lokacin raba kayayyakin jin kai ga fararen hula a kasar.

A yayin zaman kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya kan matsalar fararen hula a kasar Siriya a jiya Litinin: Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin jin kai a kasar ta Siriya Mark Lukok ya bukaci kara wa'adin raba kayayyakin jin kai ga al'ummar Siriya da suke yankunan da suke karkashin ikon kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar.

A nashi bangaren jakadan kasar Siriya a Majalisar Dinkin Duniya Bashar Ja'afari ya yi kakkausar suka kan shirun da kasashen yammacin Turai suka yi dangane da kashe fararen hula da kungiyoyin 'yan ta'adda ke yi a kasar ta Siriya; Yana mai fayyace cewa: Daga yankunan da suke karkashin kulawar sojojin Amurka ne mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish suke kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan fararen hulan Siriya.