Mutane Miliyan 15 Ne Suka Shiga Karbala Domin Ziyarar Arba'in
(last modified Tue, 30 Oct 2018 12:16:04 GMT )
Oct 30, 2018 12:16 UTC
  • Mutane Miliyan 15 Ne Suka Shiga Karbala Domin Ziyarar Arba'in

Ofishin gwamnan Karbala ne ya sanar da cewa mutanen da su ka shiga cikin birnin sun kai miliyan goma sha biyar.

Sanarwar ta ambato sakataren majalisar mulkin gundumar Karbala Mahfuz al-Tamimi yana cewa; Da akwai baki da su ka zo daga kasashen waje da adadinsu ya kai miliyan hudu, rabinsu sun fito ne daga Iran.

Mataimakin gwmanan na Karbala Ali al-mayali ya sanar da cewa da akwai jami'an tsaro da adadinsu ya kai dubu 30 da suke aikin tabbatar da tsaro a cikin birnin. Bugu da kari an ware motoci dubu 21 wadanda su ke jigilar maziyarta.

Wani rahoto ya ambaci cewa da akwai masu sa kai domin taimakawa masu ziyarar da adadinsu ya kai dubu takwas. Sai kuma 'yan jarida na kasashen waje 104 baya ga 'yan jaridar cikin gida 670.

A kowace shekara ta Allah miliyoyin mutane ne suke isa birnin Karbala domin yin ziyara.