WHO : Gurbataccen Iska Na Kashe Mutane Miliyan 7 Duk Shekara
(last modified Tue, 30 Oct 2018 17:10:45 GMT )
Oct 30, 2018 17:10 UTC
  • WHO : Gurbataccen Iska Na Kashe Mutane Miliyan 7 Duk Shekara

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar da wani rahoto wanda ke cewa mutane miliyan bakwai ke rasa rayukansu a duniya a duk shekara a sakamakon shakar gurbataccen iska.

Rahoton ya bukaci kasashen dunya dasu tashi tsaye domin dakile illolin dake tattare da shakar gurbataccen iska.

WHO ta bayyana cewa masana’antu, makamashi, hayakin ababen hawa, tara bola na cikin abubuwan dake gurbata iska sannan hakan na kawo canjin yanayin dake cutar da kiwon lafiyar dan Adam.

A shekara 2016 data gabata, yara 600,000 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutukan dake da nasaba da shakar gurbataccen iska.

Binciken ya nuna cewa shakar gurbataccen iska na kawo cututtuka kamar su canser huhu, shanyewar bangaren jiki, cututtukan dake kama zuciya da sauransu.  

A halinda ake ciki dai kungiyoyi da masu ruwa da tsaki kan sha'anin kiwan lafiya, da muhali da sufuri sun fara wani babban taro a Geneva daga yau Talata 30 ga watan Oktoba 2018 har zuwa ranar 1 ga watan Nuwamba domin tattauna hanyoyin da suka fi dacewa domin kawar da wannan matsalar a duniya baki daya.