Dubban Tunusiyawa Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Kin Jinin Yariman Saudiyya
(last modified Tue, 27 Nov 2018 17:53:28 GMT )
Nov 27, 2018 17:53 UTC
  • Dubban Tunusiyawa Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Kin Jinin Yariman Saudiyya

Dubun dubatan al'ummar kasar Tunusiya ne suka gudanar da wata gagarumar zanga-zangar kin jinin Yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya, Muhammad bin Salman saboda zargin da ake masa da hannu cikin kisan gillan da aka yi wa Jamal Khashoggi, dan jaridar kasar Saudiyyan mai adawa da salon mulkin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce dubun dubatan al'ummar kasar Tunusiyan ne suka taru a yau din nan Talata a tsakiyar birnin Tunis, babban birnin kasar a ci gaba da zanga-zangar da suke yi na nuna rashin amincewarsu da ziyarar da Yarima Muhammad bin Salman din ya kawo kasar a yau din Talata suna masu nuna cewa al'ummar kasar ba sa maraba da shi.

Rahotanni sun ce masu zanga-zangar wadanda suka taru a filin Habib Bourguiba na kasar wajen da aka faro zanga-zangar da ta kifar da gwamnatin tsohon shugaba kama-karya na kasar Zine El Abidine Ben Ali a shekara ta 2011 suna rera taken cewa: Ba a maraba da masha jini' da kuma Allah wadai da shugabannin Tunusiya da suka karbi bakuncin Bin Salman

Tun a shekaran jiya ne dai kungiyoyin kare hakkokin bil'adama daban-daban na kasar Tunusiya suka sanar da cewa za su gudanar da wani gagarumin gangami don nuna rashin amincewarsu da ziyarar da Yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya, Yarima Muhammad Bin Salman zai kawo kasar don nuna rashin amincewarsu da kisan gillan da Saudiyya ta yi wa dan jarida dan kasar Jamal Khashoggi.