Dec 12, 2018 05:24 UTC
  • MDD : Guteress Zai Halarci Taron Sasanta 'Yan Yemen

A wani mataki na karfafa wa tattaunawar neman sulhu da ake tsakanin bangarorin dake rikici a kasar Yemen, sakatare Janar na MDD, Antonio Guteres, zai je Swiden domin ganawa da bangarorin da batun ya shafa.

A ziyara da ake sa ran zai kai a gobe a Sweden, Mista Guteres zai gana da wakilan bangarorin biyu na gwamnati da kuma 'yan Houtsis, sannan daga bisani ya yi wani jawabi a yayin rufe zagayen farko na tattaunawar a cewar wata sanarwa da MDD ta fitar a birnin New York.

Wata majiyar diflomatsiyya ta shaida wa kamfanin dilancin labaren AFP, cewa ziyarar sakataren na MDD, na da manufar kara karfafa ci gaban tattaunawar wacce ake fatan sake komawa a wani waje da ba'a bayyana ba kawo yanzu a watan Janairu mai zuwa.

A makon da ya gabata ne bangarorin dake rikici a kasar ta Yemen suka fara tattaunawa bisa matsin lamba na kasashen duniya domin kawo karshen rikicin wannan kasa ta Yemen da aka shafe kusan shekaru hudu anayi wanda kuma kawo yanzu ya lashe rayukan mutane kimanin 10,000 da kuma jefa kasar cikin bala'i mafi muni a duniya inji MDD.

Tags