Dec 21, 2018 11:58 UTC
  • An Rufe Manya-Manyan Kasuwannin Kirsimeti A Kasar Jamus Saboda Barazanar Ta'addanci

Sanadiyyar barazanan tashin bom a kasar Jamus an rufe wata babbar kasuwar kirsimeti da kuma wata kasuwan a birnin Haeidi.

Kamfanin dillancin labaran Xinhua na kasar Cana ya nakalto jami'an 'yansanda na kasar Jamus suna cewa an sami sakon barazan na cewa an dana bom a wadannan wurare ne ta E-mail na wata Mujalla ta cikin gida mai suna "Focus".

Majallar ta kara da cewa wadannan sakonni na barazana sun tada hankalin mazauna da kuma jami'an tsaro na jihar Schleswing-Holstein.

Labarin ya kara da cewa an rufe wasu manya manyan gine-gine a yankunan Flensburg, Lubeck da kuma Itzehoe duk da cewa babu wani abu da aka gane mai yin barazana ga rayukan mutane a cikinsu. 

Wasu kafafen yada labarai sun bayyana cewa jami'an tsaro suna kokarin gano dangantakar da ke tsakanin wadannan sakonni na barazana da ake yi ta aikawa wannan mujallar.

 

Tags