Jan 24, 2019 07:14 UTC
  • Wasu Tagwayen Motoci Shake Da Bama-Bamai Sun Tarwatse A Somaliya

Kafafen watsa labarai na kasar Somaliya sun sanar da cewa a marecen jiya Laraba wasu tagwayen motoci shake da bamai-bamai sun tarwatse a Magadushu babban birnin Kasar

Kamfanin dillancin labaran Pars ya nakalto kafafen watsa labarai na kasar Somaliya na cewa a marecen jiya Laraba wasu tagwayen motoci shake da bamai-bamai sun tarwatse a gaban wani Banki na Magadushu babban birnin Kasar.

Tuni Kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab mai alaka kut da kut da kungiyar Alka'ida ta dauki alhakin kai harin.

Kungiyar Ashabab din ta ce tashin Bam din ya hallaka sojojin Somaliya guda shida.

Tun a shekarar 2007 ne , kungiyar ta Ashabab ke kokarin kawar da gwamnatin kasar Somaliya, to saidai a shekarar 2011,Sojojin Somaliya tare da hadin gwiwar dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka sun samu nasarar fatattakar mayakan na Ashabab daga Magadushu babban birnin kasar da kuma wasu manyan buranan kasar.

A halin da ake ciki, har yanzu kungiyar ta Ashabab na ci gaba da rike da wasu kauyukan kasar.

Tags