Rasha Da China Sunyi Tir Da Sabbin Takunkuman Amurka Kan Venezuela
Kasashen China da Rasha sunyi allawadai da sabbin takunkuman da Amurka ta kakaba wa kasar Venezuela.
Rasha ta bakin kakakin fadar shugaban kasar, Dmitri Peskov, danganta lamarin ta yi da shishigin da wuce gona da iri, tare da shan alwashin kare kaddarorinta ta hanyoyin da dokokin kasa da kasa suka tanada, da kuma karfin da take dashi.
Ita ma a nata bangare kasar China, wacce ke zaman kawar venezuela ta kud da kud, ta yi tir da allawadai da takunkuman Amurka kan kasar ta Venezuela, inda a cewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta China, Geng Shuang, takunkuman zasu kara dagula al'amurran rayuwar al'ummar Venezuela, tare da cewa wadanda suka kisa rikicin su ne keda alhakin abunda zai biyo baya.
Dama dai kafin hakan shugaban kasar ta Venezuela, Nicolas Maduro, ya yi fatali da takunkuman yana mai dangantasu dana zalinci.
Ko baya ga kasashen Rasha da China, Shugaba Maduro na ci gaba da samun goyan bayan kasashen, Koriya ta Arewa, da Turkiyya da kuma Cuba, a yayin da wasu kasashen turai da suka hada da Faransa, Jamus, Spain, Burtaniya, Portugal, da Holland suka baiwa shugaba Maduro wa'adin kwanaki takwas na ya kira zabe ko kuma su amince da madugun adawa na Venezuelar, Juan Guaido, a matsayin shugaban kasar na riko.
A jiya Litini ne Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan kamfanin man fetur na kasar Venezuela, PDVSA, bayan da a cen baya ta amince da Juan Guaido wanda ya ayyana kansa shugaban Venezuellar a mastayin halataccen shugaban kasar.