Venezuela Ta Bukaci Goyon Bayan MDD
(last modified Thu, 21 Feb 2019 18:21:38 GMT )
Feb 21, 2019 18:21 UTC
  • Venezuela Ta Bukaci Goyon Bayan MDD

Wakilin kasar Venezuela a MDD ya bukaci jakadodin kasashen Duniya 46 na majalisar da suka gudanar da zama da nufin tabbatar da alkawarin da Majalisar ta dauka na nuna adawa da barazanar kai harin soja a kan kasar

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya habarta cewa wakilin  kasar Venezuela a MDD ya aike da wasika zuwa saktare janar na MDD António Guterres inda ya nuna damuwar Caracas a game da barazanar amfani da karfin soja a kan kasar, wanda ya ce yin hakan shi ne tabbacin karya dokokin Majalisar Dunikin Duniya.

Har ila yau wakilin na Venezuela ya bukaci kasashen Duniya  46 na su gudanar da zama a gobe juma'a, domin gudanar da bincike kan wasikar da kasarsa ta aikewa majalisar.

Harwa yau cikin wasikar, gwamnatin kasar  Venezuela ta nuna goyon bayanta na warware rikicin siyasar  kasar ta hanyar tattaunawa da sulhu gami da tabbatar da gaskiya a tattaunawar.

Wakilin kasar Venezuelan ya ce ya yi imanin cewa saktare janar na MDD António Guterres nada karfin da zai kawo karshen rikicin kasar ta hanyar sulhu da kuma hana aukuwar yaki a kasar.

A ranar 18 ga wannan wata na favrayu ne,a ci gaba da barazar da yake yiwa kasar ta  venezuela, Shugaba Trump ya bayyana cewa  matukar dai shugaba Madoro bai sauka daga kan karagar mikin kasar ba, to Amurka na iya daukan matakan da take ga   ya dace domin kawo karshen gwamnatin ta Nicolas Madoro a kasar ta Venuzuela.