Feb 22, 2019 19:20 UTC
  • An Tsawaita Lokacin Tsare Dan Kasar Amurka Da Ake Tuhuma Da Leken Asiri A Rasha

Ma'aikatar sharia'a a kasar Rasha ta bukaci a ci gaba da tsare dan kasar Amurkan nan wanda gwamnatin kasar take tuhuma da aikin leken asiri.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto majiyar shari'a ta kasar Rasha tana bada sanarwan cewa an tsawaita lokacin tsare paul Whelan wanda a halin yanzu yake tsare a cikin gidansa a kasar ta Rasha don sauraron shari'a.

Labarin ya kara da cewa kotu ta bukaci a ci gaba da tsare Paul har zuwa ranar 28 ga watan Mayu na wannan shekara ta 2019. 

Mr Paul Whelan tsohon sojan Amurka ne wanda kuma yake rike da Passpor na kasashen Britania, Canada da kuma Island. Kuma jami'an tsaro a kasar Rasha suna tsare da shi a masaukinsa tun ranar 28 ga watan Decemban shekara ta 2018 da ta gabata.

A zaman sauraron shari'arsa ta farko a cikin watan Decemban shekara ta 2018, kotun da ta saurari kasar ta bukaci a ci gaba da tsare shi har zuwa ranar 28 ga watan Febrerun da muke ciki. 

Sergei Ryabkov, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya yi allawadai da shigar kasar Rasha wanda Paul Whelan ya yi, da kuma ayyukan da ya fara yi bayan shigarsa kasar, wanda ya nuna cewa kamar ya zo ne don aikin leken asiri.   

Tags