‘Yan Ci-rani 84 Sun Bata A Tekun Libya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i4585-yan_ci_rani_84_sun_bata_a_tekun_libya
kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya ta ce bakin haure kimanin 84 ne suka bace bayan da kwale-kwalen da suke ya kife a tekun Libya.
(last modified 2018-08-22T06:58:12+00:00 )
May 01, 2016 01:20 UTC
  • 'yan ci rani a teku
    'yan ci rani a teku

kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya ta ce bakin haure kimanin 84 ne suka bace bayan da kwale-kwalen da suke ya kife a tekun Libya.

Kafin hakan dai wani babban jirgin ruwan Italiya ya yi nasarar ceto rayuwar wasu bakin hauren 26 daga cikin wadanda kwale kwalen ya kife da su a teku a ranar Juma'a data gabata.

Yanzu haka kuma Jami'an agaji da Sojojin ruwan Italiya na ci gaba da neman sauran mutanen da suka nutse a teku kusa da Lampedusa.

Bayanai sun nuna cewa galibin bakin hauren da aka yi nasarar cetowa 'yan yammacin Afirka ne, koda yake hukumomin Italia na kokarin tantance kasashen ‘Yan ci-ranin.

Al'kaluma sun nuna cewa kimanin bakin haure dubu 27 ne suka isa Itaiya ta kwale-kwale a bana kawai.