Amurka Na Shirye Don Sassautawa Libya Takunkumin Sayan Makamai
Gwamnatin Amurka ta ce a shirye take wajen sassauta takunkumin sayan makamai na MDD ga kasar Libya, domin taimakawa gwamnatin hadaka ta kasar yaki da kungiyar (ISIL).
Wani babban jami'in Amurkar ya ce idan dai gwamnatin Libya ta bayyana dalla-dalla irin kayan da take bukata don yakar 'yan ta'adan, to kwamitin tsaro na mdd zai duba wannan bukata da mahimmanci.
A cikin shekara 2011 ne Mdd ta kakaba takunkumin sayan makamai ga kasar ta Libya.
Wani jami'in gwamnatin Libya ya bayyana a jiya Alhamis cewa 'yan ta'adan IS sunyi nasara kwace ikkon yankin Abou Grein mai muhimmanci a yammacin Kasar.
Kungiyar IS dai tayi amfani da rikicin da kasar Libya ta tsunduma wajen yin kaka-gida a wasu sassan kasar tun bayan guguwar neman sauyi datayi awan gaba da mulkin tsohon shugaban kasar mirigayi kanal Ghadafi a shekara 2011.