Ana Taro A Vienna Kan Halin Da Ake A Libya
May 16, 2016 05:36 UTC
Yau Litinin ministocin harkokin wajen kasashen turai dana Amurka dama na kasashe makoftan Libya na taro a Vienna, domin tattauna halin da ake ciki a kasar Libya.
Kasar Libya dai na fama da rikicin siyasa da kuma barazanar kungiyoyin 'yan ta'ada irinsu (IS) tun dai bayan guguwar neman sauyi data yi awan gaba da mulkin tsohon shugaban kasar mirigayi kanal Ghadafi.
Taron dai maida hankali ne kan yadda za'a tainmakawa kasar Libya samun gindin zama wajen tabbatar da zamen lafiya, kamar yadda shugaban diflomatsiyan kasar Italiya Paolo Gentiloni dake jagorancin taron ya sanar ga manema labarai.
Tags