Shugaban Azhar Yana Goyon Bayan Hadin Kan Shi'a Da Sunna.
Shugaban Jami'ar Azhar ta Masar ta ce; Mazhabobin Shi'a da sunna tamkar fika-fikai biyu ne na musulunci, dole ne su ku kara kusantar juna.
Shugaban Cibiyar Azhar ta Masar Sheik Ahmada Tayyib wanda ya ke halartar wani taro a kasar Indonesia, ya ce; Mabiyu mazhabobin shi'a da sunna tamkar fika-fikai biyu ne na musulunci don haka wajibi ne su zama masu kusantar juna.
Shugaban na Azhar ya kuma kirayi malaman addinin musulunci na Masar da kuma Indonesia da su zama masu masu farfado da ruhin musulunci na asali wanda ya ke cike da jin kai da tausayi.
Bugu da kari shehun na Azhar ya ce; abubuwan da aka hadu akansu a tsakanin shi'a da sunna sun fi wadanda ake da sabani akansu.
Har ila yau, Shehun na Azhar ya ce bai kamata a baiwa makiyan addinin musulunci damar da za su haddasa sabani a tsakanin musulmin ba.