Kamaru : Hare-haren Kunar Bakin Wake Sun Kashe Mutane 6
Feb 10, 2016 08:27 UTC
-
wani sojan kamaru a arewa mai nisa
Akasarin wadanda hare-haren suka rutsa dasu yara ne.
Rahotanni daga kamaru na cewa mutane shida ne suka rasa rayukan su, a wasu jerin hare-haren kunar bakin wake a kwauyan Nguetchewe dake yankin arewa mai nisa na kasar.
Hare-haren da aka kai a wannan kauyen dake kan iyaka da Najeriya sun kuma sanadin jikkata wasu mutane akalla 30 a cewar wasu majiyoyin tsaro.
An dai kai harin ne kan wasu masu zaman makoki a kauyen inda wasu bayanai ke cewa wadanda suka jikkatan zasu iya kai 50.
kawo yanzu babu wata kungiya data dau alhakin kai wadanan hare-haren, aman so tarin yawa akan danganta su da kungiyar nan da aka fi sani da Booko Haram.
Tags