Majami'ar Birnin Landan Ta Shirya Buda Baki
(last modified Mon, 27 Jun 2016 05:07:35 GMT )
Jun 27, 2016 05:07 UTC
  • Majami'ar Birnin Landan Ta Shirya Buda Baki

Daya daga cikin manyan majami'oin mabiya addinin kirista mafi dadewa a birnin landan an kasar Burtaniya ta kirayi taron buda baki.

jaridar International News ta bayar da rahoto a shafinta na yanar gizo cewa, majami'ar Start James ta gayyaci daruruwan mutane zuwa taron buda baki, da suka hada da musulmi da ma wadanda ba musulmi ba, da nufin kara kusanto da fahimtar juna tsakaninsu da mabiya addinin muslunci.

 

Magajin garin birnin Landan Sadiq Khan, wanda shi ne babban bako mai jawabi a wurin, ya bayyana cewa aiki ne da ya rataya a kan musulmi da wadanda ba musulmi ba, musamman ma dai mabiya addinai da aka safkar daga sama, da su yi aiki tare da wajen tabbatar da adalci da 'yan adamtaka, da jin kan raunana, da taimakon talkawa marassa galihu a dukaknin bangarori na rayuwarsu, wanda kuma wannan shi ne hikimar azumi.

 

Ya ce abin takaici ne yadda aka wayi gari wasu 'yan tsiraru daga cikin musulmi suna bata wa musulunci suna ta hanyar munanan ayyukansu na ta'addanci, sakamakon akidun da suke dauke da su wadanda ba su cikin koyarwar addinin muslunci, domin kuwa shi musulunci addinin zaman lafiya da fahimtar juna ne tsakaninsa da sauran addinai, a kowane lokaci muslunci yana fifita hanyoyin na hikima da hankali wajen isar da sakonsa sabanin akidar 'yan ta'adda.

 

Shi ma a nasa bangaren Ryod Lossy, wanda shi ne ya dauki nauyin shirya buda bakin ya bayyana cewa, wannan babbar dama ce gare su domin kara samun kusantar juna tsakaninsu da musulmi, da kuma kara fayyace ma sauran mabiya addinin kirista da sauran addinai cewa zaman lafiya da juna shi ne manufar addinai na kiristanci da muslunci, kuma babu ko daya daga cikin wadannan addinai guda biyu da ya yarda da zaluntan dan adam.