Yemen : HRW Ta Nemi Ayi Bincike kan Harin Kawancen Saudiyya
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa, Human Rights Watch (HRW), ta nemi da a gudanar da bincike kan hare haren da kawancen da Saudiyya ke jagoranta kan wasu cibiyoyin tattalin arziki a kasar Yemen.
kungiyar ta Human Rights Watch (HRW) ta ce wadanan hare -haren zasu iya zama laifukan yaki.
A wani rahoto data fitar yau Litinin kungiyar ta kiyasta hare-hare sama har guda 17 da kawacen ya kai a baya bayan nan wanda ya shafi cibiyoyin tattalin arziki na fararen hula 17 da suka hada da masana'antu da wuraren adanon kayayakin kasuwanci da cibiyoyin wutar lantarki wanda suka yi sanadin mutuwar fararen hula 130.
kungiyar ta ce babban hare-haren sun kasance babban kalubale ga tattalin arzikin Yemen don haka a gudanar da sahihin bincike ba tare da nuna rashin bambanci ba cikin gaggawa a wannan kasar ta Yemen.