Libiya : Jiragen Yakin Amurka Sun Kashe Mutane 40
Akasarin wadanda aka kashe a birnin Sabrata 'yan Tunusia ne.
Amurka ta tabbatar da cewa jiragen yakin saman ta sun kai hari kan wani sansanin hora da 'yan ta'adan (IS) a kasar Libiya.
Harin wanda aka kai a wannan juma'a yayi sanadin mutuwar mutane sama da 40 kamar yadda mahukunatan kasar ta Libiya suma suka tabbatar.
Amurka dai na zaton cewa ta kashe wani babban kwamadan kungiyar (IS) mai suna Noureddine Chouchane dake da hannu a hare-haren ta'adanci biyu da aka kai bara a kasar Tunusiya.
Wani jami'in karamar hukumar birnin Sabrata inda aka kai harin ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa dukkan wadanda lamarin ya rusa dasu 'yan asalin kasar ta Tunusiya ne, wanda bisa ga dukkan alamu a cewar sa membobin kungiyar (IS) ne.