-
Rasha : Gwamnan Kemerovo Ya Yi Murabus
Apr 01, 2018 06:01Gwamnan jihar Kemerovo, a Rasha ya yi murabus daga mukaminsa, mako guda bayan mummunar gobara data yi sanadin mutuwar mutane 64 a wani shagon sayar da kayayakin masarufi a yankin Siberiya.
-
Vanezuella : An Cafke Manyan 'Yan Sanda 5 Biyo Bayan Gobara Gidan Yari
Apr 01, 2018 05:46Rahotanni daga Venezuella na cewa an cafke wasu manyan jami'an 'yan sanda biyu da ake zargi da hannu a rikici da kuma mummunar gobara data yi ajalin fursunini da dama a yankin Carabobo.
-
'Yan Houthi: Idan Da Iran Tana Ba Mu Makamai, Da Yanzu Mun Kama Riyadh
Apr 01, 2018 00:35Shugaban Kwamitin Juyin Juya Hali na kasar Yemen, Mohammed Ali al-Houthi, ya musanta zargin cewa Iran tana ba wa dakarun kasar Yemen makamai a fadar da suke yi da sojojin wuce gona da iri na Saudiyya yana mai cewa idan da a ce Iran tana ba su makamai, to da yanzu sun kame birnin Riyadh.
-
Faransa Ta Kori Wasu Mutane 20 Daga Cikin Kasar
Mar 31, 2018 14:39Ma'aikatar cikin gidan Faransa ta sanar da korar mutane 20 da ta zarge su da tsattsauran ra'ayi cikin shekarar 2017
-
Tawagar MDD Ta Fice Daga Laberiya
Mar 31, 2018 06:06Bayan shafe shekaru 14, na aikin wanzar da zaman lafiya, tawagar MDD ta (Minul) ta fice daga kasar Laberiya a jiya Juma'a.
-
Guterres Ya Bukaci A Gudanar Da Bincike Kan Kisan Da Isra'ila Ta Yi Wa Palastinawa A Gaza
Mar 31, 2018 02:23Babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bukaci da a gudanar da bincike dangane da kisan da sojojin Isra'ila suka yi kan Palastinawa a jiya Juma'a a yankin Gaza.
-
Aljazeera: Bin Salman Ya Gana da Jagororin Manyan Kungiyoyin Yahudawa A Amurka
Mar 31, 2018 02:13Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a ziyarar da yake gudanarwa a kasar Amurka, yariman saudiyya mai jiran gado Muhammad Bin Salman ya gana da jagororin manyan kungiyoyin yahudawa a Amurka, masu tallafa wa Isra'ila.
-
'Yan Ta'adda Sun Kashe Ma'aikacin Kungiyar Bada Agaji Ta Red Cross A Somaliya
Mar 30, 2018 06:48Kungiyar bada agajin gaggawa ta Red Cross ta sanar da kashe ma'aikacinta guda a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar Somaliya a wani harin wuce gona da iri da aka kai kan motar da ke dauke da shi.
-
Trump: Za Mu Fice Daga Kasar Siriya, Nan Ba Da Jimawa Ba
Mar 30, 2018 00:34Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa 'nan ba da jimawa' ba Amurka za ta fice daga kasar Siriya, 'yan awanni bayan da Ma'aikatar tsaron kasar Amurkan ta sanar da cewa akwai bukatar sojojin Amurkan su ci gaba da zama a Siriyan.
-
Rasha Ta Kori Jami'an Diflomatsiyan Amurka 60
Mar 29, 2018 13:51Kasar Rasha ta kori jami'an diflomatsiyan Amurka guda 60, da kuma rufe karamin ofishin jakadancin Amurkar na birnin Saint-Pétersbourg, a mastayin maida martani kan korar nata jami'an da Amurkar ta yi biyo bayan zargin yunkurin kashe wani tsohon jami'in leken asirin Rashan da 'yarsa a Birtaniya.