-
Kotun ICC Ta Daure Tsohon Shugaban Sabiyawa, Karadzic Shekaru 40
Mar 25, 2016 00:23Kotun duniya mai shari'ar manyan laifukan yaki ta yanke wa tsohon shugaban Sabiyawan Bosniya Radovan Karadzic hukunci daurin shekaru 40 a gidan yari saboda samunsa da hannu dumu dumu cikin kisan kiyashi da aka yi wa wasu musulmai yanki Srebrenica a shekarar 1995.
-
Kungiyar Boko Haram ta fitar da Wani sabon faifan bidiyo
Mar 24, 2016 12:42Kungiyar Boko Haram ta fitar da wani sabon bidiyo da ke tabbatar da cewa shugaban Kungiyar Abubakar Shekau na raye.
-
Firaministan kasar Belgium ya ki amincewa da murabus din ministocinsa biyu
Mar 24, 2016 10:50Ministocin cikin gida da na shara'ar kasar Belgium sun meka takarar murabus din su ga Firaminstan kasar sakamakon tagwayen hare-haren ta'addancin da aka kai ranar talatar da ta gabata.
-
Clinton Ta Cacaki Tsarin Turai Na Yaki Da Ta'adanci
Mar 23, 2016 23:24Tsohuwar sakatariyyar gwamnati kana 'yar takarar shugaban kasa a Amurka, Hillary Clinton ta soki tsarin kasashen Turai da jan-kafa wajen yaki ta'adanci.
-
Hukumomin Belgium Sun Sanar Da Gano Wadanda Suka Kai Harin Brussels
Mar 23, 2016 05:57Kafafen watsa labaran kasar Belgium sun sanar da cewa jami'an tsaron kasar sun sami nasarar kama mutum na uku da ake zargi da hannu cikin harin ta'addancin da aka kai babban filin jirgin saman Zaventum da ke birnin Brussels na Belgium da kuma wata tashar jiragen kasa a jiya bayan sun gano mutane biyun da suka kai harin.
-
Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Yi Allawadai Da Harin Brussels
Mar 23, 2016 00:20Kungiyar kasashen musulmi ta yi Allawadai da harin da aka kai a birnin Brussels na kasar Belgium a jiya Talata, tare da bayyana hakan da cewa aiki ne na ta'addanci.
-
Kotun Manyan Laifuka Ta Duniya Ta Yanke Wa Tsohon Mataimakin Shugaban Congo Hukunci
Mar 23, 2016 00:08Kotun manyan laifuka ta duniya ta yanke hukunci kan tsohon mataimakin shugaban Congo Jean Pierre Bemba, bisa laifin aikata cin zarafin dan adam a lokacin da yake jagorantar kungiyar 'yan tawaye a 2002 zuwa 2003.
-
Kungiyar ISIS ta dauki nauyin kai harin Brussels
Mar 22, 2016 13:22Kungiyar 'yan ta'adan ISIS ta dauki nauyin kai harin Brussels da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 30 tare da raunana wasu sama da 200 a wannan Talata.
-
Wasu Bama-Bamai Sun Fashe A Filin Jirgin saman Birnin Brussels, Na Kasar Belgium.
Mar 22, 2016 06:24Rahotanni daga kasar Belgium sun bayyana cewar wasu bama bamai guda biyu sun fashe a filin jirgin sama na Zaventem da tashar jirgin kasa na Malbeek da ke birnin Brussels, babban birnin kasar Belgium din, inda wasu rahotanni suka ce alal akalla mutane 13 sun mutu wasu da dama kuma sun sami raunuka.
-
Rasha Ta Gargadi 'Yan Tawayen Syria Dangane Da Karya Yarjejeniyar Tsagaita Wuta
Mar 21, 2016 13:37Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta bayyana cewa, ta bayar da wa'adi zuwa gobe Talata 22 ga watan Maris ga Amurka, kan ta bayyana matsayinta dangane da masu tayar da kayar baya a Syria da suka ki yin aiki da yarjejeniyar dakatar da bude wuta, idan kuma ba haka ba Rasha za ta dauki mataki a kansu.