Aug 23, 2016 05:14 UTC

shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka domin samun tsira daga Bata,

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta Yau, ta yaya zai kasance dabi'ar hakuri a matsayin neman taimakon Allah madaukakin sarki? Domin shi hakuri Jihadi ne  daga Zatin Dan Adam, domin amsa wannan tambaya za mu koma cikin Nassosi na Nauyaya guda biyu wato Alkur'ani mai tsarki da kuma tafarkin Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka, amma kafin nan bari mu saurari wannan.

*********************************Musuc****************************

Masu Saurare Hakika, Allah tabarka wa ta'ala ya umarce mu da neman taimako ta hanyar hakuri a cikin ayoyi da dama na Alkur'ani, daga cikin su Aya ta 153 cikin suratu Bakara inda Allah Tabaraka wa ta'ala ke cewa:(Ya Ku wadanda kuka bada gaskiya, Ku nemi taimako da Hakuri da salla.Hakika Allah yana tare da masu hakuri) suratu Bakara Aya ta 153,Masu saurare kamar yadda wannan Aya mai tsarki ta bayyana Hakika Allah yana tare da masu Hakuri, ma'ana dabi'antuwar Mumuni da dabi'ar hakuri zan kasance masa hanya ta rabauta na samun kusanaci da Mahalicinsa, ya bashi nasara a kan bayinsa kuma ya taimake sa madaukakin sarki.

Masu Saurare Neman taimako da Hakuri, Hakika yana nufin neman Taimako ga Allah madaukakin sarki, domin shi Allah shine ya horewa bawansa Ni'imar Hakuri, idan ya dogara da shi, zai kasance a hakika dogaro ga Allah madaukakin sarki ne. kamar yadda idan Bawa ya nemi taimako da wannan Ni'ima ta Ubangiji  ya rabauta da taimako na kari daga Allah madaukakin sarki wacce za ta yi masa Jagora wajen cimma manufarsa, kuma ribar hakurinsa shine Hakika Allah yana tare da masu Gaskiya. A cikin Littafin Misbahul Shari'a cikin wani Hadisi mai tsaho ,Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(duk wanda yayi marhabi  wani bala'I da aka jarrabe sa da shi, ya kuma yi hakuri cikin Nutsuwa da kariya, shi yana daga cikin zababbu, watau zababbu daga cikin mumunai, kuma nasibinsa ko rabonsa shine fadar Allah madaukakin sarki, (Allah yana tare da masu hakuri).Allama muhamad bn Mas'oud Al'ayyashi cikin Tafsirinsa wanda ake kira da Tafsiriu Ayyashi ya ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Muhamad Albakir (a.s), shi dai wannan hadisi yana shiryar da mu cewa Hakika neman taimako da Hakuri, nauyi na Ubagiji da ya rataya a kan ko wani Mutum kuma shi ke tabbatar da hakikanin bautar Allah madaukakin sarki da kuma riko da wilayar waliyansa amincin Allah ya tabbata a gare su.Imam (a.s) ya fadawa daya daga cikin Sahabansa:Ya Fudail ya isar da wannan sako ga wand aka hadu da shi daga cikin mabiyanmu da farko ka isar da sakon sallamarmu a garesu sannan ka ci musu:Ni ba zan  wadatar da ku da komai a wajen Allah face da tsoron Allah ba, ku kiyaye harshenku, ku kuma rike hannayanku, kuma na hore ku da hakuri da salla,(Hakika Allah yana tare da masu hakuri) wato Abinda Imam (a.s) yake nufi da wannan hadisi shine matukar Mutun ba ya tsoron Allah kuma ba ya bin dokokin Allah yayi aiki da umarnin Allah da kame da abinda Allah ya hane shi da shi wulayarsa ba za ta amfana masa komai ba.

***********************Musuc******************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, A ci gaban shirin za  mu fara da kisser bani Isra'ila inda labarin Alkur'ani mai girma ke tabbatar da cewa neman taimakon Allah ta hanyar dabi'antuwa da dabi'ar hakuri  ta kan kai ga cimma Nasarar ubangiji ga masu hakurin, kamar yadda ya wakana ga Bani Isra'ila a yayin da Allah madaukakin sarki ya tserar da su daga sharin Shugabanin  masu dagawa ya kuma kadar musu da kasar, A cikin suratu A'arafi Aya ta 128 Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Musa ya ce da Mutanansa. Ku nemi taimakon Allah, ku kuma yi hakuri, Hakika Kasa ta Allah ce, Yana gadar da ita ga wanda ya so daga bayinsa.Kyakkyawan Karshe kuwa yana ga masu tsoron Allah).