Jan 25, 2018 17:23 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,tambayarmu ta yau shin ayoyin kamalar addinin da cikar ni'ima suna shiryarwa ne zuwa ga shugabancin Ali(a.s) ne ko kuma dukkanin shugabanin shiriya 12 na iyalan gidan anabta tsabakaka?  kafin amsa wannan tambaya sai a dakacemu da wannan.

************************Musuc****************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, da farko za mu fara ishara zuwa sababin nuzulin wannan aya da ta sauka a hajjin ma'aikin Allah (s.a.w.a) ta karshe, A cikin suratu ma'ida Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Ya kai Wannan Manzo, ka isar da abin da aka saukar gare ka daga Ubanganka, idan kuma ba ka aikata (haka) ba, to ba ka isar da sakonsa ba, Allah kuma zai kiyaye ka daga (sharrin) mutane. Hakika Allah ba ya shiryar da mutane (wadanda suke) kafirai). Suratu Ma'ida aya ta 67, yin nazari cikin wannan aya mai albarka, zai shiryar da mutum munsifi tun kafin komawa zuwa ga riwayoyin da suke bayyani kan sababin nuzulin wannan aya, akwai umarnin ubangiji mai mahimanci da ya sauka a kan ma'ikin Allah cikamakin annabawa (s.a.w.a), sannan kuma ya umarci isar da wannan sako ga mutane, wannan umarni na ubangiji na ishara da mahiman abu cikin tushen risalar muhamaddiya, a yayin da rashin isar da wannan sako yana nufin ,rashin isar da tushen risala, ta hanyar da wannan sako ne, addinin ubangijin na karshe zai karfafa.

A bayyane yake, sigar ayar ta nuna cewa hakika Annabin rahama tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya kasance ya nada fargaba na bayyana wannan umarni mai mahimanci saboda wani martani da ya kasance yana tunanin zai fuskanta daga wa'insu, domin hakan ne ma Allah ta'ala yayi alkawarin karesa daga mutane kuma ba zai taba barin wannan martani da yake tunanin ma'aikinsa zai fuskanta ya auku a yayin da yake son isar da wannan sako na ubangiji tabaraka wa ta'ala.kuma tushen wannan martani na rashin karbar gaskiya shi ne  kafiran da ba suyi imanin gaskiya ba da sakon Annabin Rahama (s.a.w.a) ko da kuwa a zahiri sun bayyana musulincinsu, domin haka ne ma Allah madaukakin sarki ya kamala ayar da cewa:( Hakika Allah ba ya shiryar da mutane (wadanda suke) kafirai) abin tambaya nan, wani al'amari ne aka umarci ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya isar da shi?kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari wannan.

*************************Musuc******************************

Masu saurare, an ruwaito hadisai da dama daga bangarorin shi'a da sunna kamar yadda allama Aminy cikin mausu'arsa AlQadir da waninsa daga cikin malimai na sunna da shi'a suka ruwaito, cikin binciken da suka yi sun tabbatar da cewa wannan aya ta sauka a waki'ar Qadir, inda ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya bayyana khilafancin shugaban muminai Aliyu bn Abi talib (a.s) kuma majibincin al'amuran musulmi bayansa,amma wannan umarni bai takaita ba kawai ga shugabancin Imam Ali (a.s) shi kadai, saidai ya kumshi khilafancin dukkanin shugabanin shiriya 12 na iyalan gidan anabta tsarkaka,saboda  kasancewar wannan umarni nada alaka da iyalan gidan Annabin Rahama Muhamadu Dan Abdullahi (s.a.w.a), hakika Sadikul Amin (s.a.w.a) ya ji tsoron bayyana wannan sako na Ubangiji  saboda tsoron martanin da zai fuskanta wanda ya samo asali daga kabilanci irin na lokacin jahiliya da ya nuna rashin amincewa na kasancewar Anabta da khilafanci a kabila guda daga cikin kabilar kuraishawa, wato(kabilar Bani Hashim), wannan shi ne abinda ya fito daga bakukunan da dama daga cikin al'ummar kuraishawa daga cikin su har da manyan sahaban Annabin Rahama (s.a.w.a) kamar yadda aka ruwaito cikin litattafan tarihi masu inganci.hakika al'ummar kuraishawa ba ta kasance ta karbi wannan al'amari ba  ko da kuwa wannan umarni daga wajen Allah mai hikima ya zo.hakika Kuraishawa sun bukaci rarraba makamai da matsayi a sassanta kamar ya kasance a kan jagorancin kaba'a, kamar yadda ya zo a cikin litattafai masu inganci,haka nan ya kasance suna  jiran wannan lamari na kakkasa jagoranci a cikin al'umaran Addinin Ubangiji duk da cewa Alkur'ani mai girma ya bayyana cewa Allah madaukakin sarki shi ya san inda yake sanya sakonsa. To saidai shugabanin kuraishawa ba su gushe suna kalubalanta wannan lamari ba, domin haka ne ma Annabin Rahama ya yi fargabar bayyana wannan umarni na ubangiji  dangane da iyalan gidansa tsarkaka a gare su ba saboda har zuwa wannan lokaci akwai jayayya da ganin fifiko tun irin na jahiliya a zukatan wasunsu.

Ba ya ga wannan, malimai sun bayyana cewa kasancewar (s.a.w.a),mai tausayi ga mutane, domin haka ya ji musu tsoron mumunan sakamako na saukar azabar ubangiji, idan har ya isar da wannan umarnir Allah a game da iyalan gidansa tsarkaka, wasu mutane suyi masa  tawaye , kamar yadda ya wakana, kamar kuma yadda aka yi ishara cikin ayoyin farko na suratul-Mi'iraj kan abinda ya biyo baya bayan isar da sakon umarnin Allah a waki'ar Qadir kamar yadda za mu nakalo muku nan gaba.

**********************Musuc***************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, a cikin tafsirin Majma'ul bayaan, an nakalto hadisi daga Hakim Haskani Ashafi'I daga shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) daga ma'aifansa amincin Allah ya tabbata a gare su ya ce:( yayin da ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya bayyana Imam Ali(a.s) a matsayin majibincin Al'amuran musulmi bayansa, ya ce:(duk wanda na kasance majibincin al'amuransa to Ali shi ne majibincin al'amuransa, wannan labari ya janyo kananen maganganu a cikin gari, har takai ga Nu'uman bn Haris Alfahry zuwa wajen ma'aikin Allah (s.a.w.a) yace masa ka umarce mu mu shaida cewa babu wani abin bauta da gaskiya face Allah kuma hakika kai ma'aikin Allah ne, ka umarce mu da yin jihadi, aikin hajji, yin azumi, tsai da salla da kuma bayar da zakka, mun amince, sannan ba ka aminta da wannan ba har sai da ka nada mana wannan yaro sannan ka ce: duk wanda na kasance majibincin al'amuransa, Ali majibincin al'amuransa ne, shin wannan daga gareka ne, ko kuma umarni ne daga wajen Allah? Sai ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce: na rantse da Allah wanda babu abin bauta face shi, wannan umarni daga Allah ne, sai Nu'uman bn Haris ya juya yana cewa wallahi idan wannan ya kasance gaskiya ne daga Allah ne, Allah ya saukar mana duwatsun azaba daga sama, sai Allah madaukakin sarki ya jefe sa da dutsi a kansa ya hallaka, sai Allah ta'ala ya saukar da wannan aya:(Mai tambaya ya yi tambaya game da azaba mai afkuwa) suratu Ma'ariji aya ta farko da wannan masu saurare, ya bayyana cewa hakika ayar (Ya kai Wannan Manzo, ka isar da abin da aka saukar gare ka daga Ubangijinka) tana kafa dalili a kan mahimancin al'amarin shugabanci da wulaya, kuma ta hanyarsa ne addini na gaskiya ke karfafa. Hakika maliman tarihi sun ruwaito hadisai na bangarori daban daban da cewa sakon da ma'aiki (s.a.w.a) ya isar yayin saukar da wannan aya ta kumshi khilafancin Imam Ali (a.s) bayansa cikin Khodubar ranar Qadir da kuma bayyana shugabancin iyalan gidansa tsarkaka a hadisin sakalain da ya kasance wani bangare ne na wannan khoduba, kuma da wannan ne, ayar ta kasance hujjar Ubangiji na shugabancinsu (wato limaman shiriya 12 na iyalan gidan anabta tsarkaka) baki daya, ba wai Imam Ali (a.s) shi kadai ba, kuma wannan shi ne abinda za mu nakalto muku a shiri mai zuwa da yardar Allah ta'ala.

**************************Musuc***************************

Masu saurare ganin lokaci da aka debawa shirin ya zo karshe, a nan za mu dakata, sai kuma a maku na gaba da yardar allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimamakawa shirin har ya kamala musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da jagoranci shirin nike muku fatan alheri, wassalama alekum.