Jan 25, 2018 17:21 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,tambayarmu ta yau yaya za mu iya kafa hujja da Ayar wulaya ta cikin suratul-wulaya wacce Allah madaukakin sarki ke cewa (Allah a hakika shi ne mai jibintar al'amuranku) dangane da shugabancin iyalan gidan anabta tsarkaka? Kuma mu za mu iya amfana ta hanyar akida daga wannan aya? , kafin hakan sai a dakacemu da wannan.

************************Musuc****************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ayar wulaya ita ce aya ta 55 da kuma aya ta 56 cikin suratu ma'ida, Allah madaukakin sarki ya ce:(Allah a hakika shi ne Mai jibintar al'amarinku da manzonsa da kuma wadanda suka bada gaskiya, wadanda suka tsai da salla da ba da zakka a yayin da suke cikin ruku'i*Duk kuwa wanda ya sa Allah a gaba a kan al'amarinsa da manzonsa da kuma wadanda suka ba da gaskiya, to hakika rundunar Allah su ne masu rinjaye) suratu ma'ida aya ta 55 da ta 56. Masu saurare cikin wannan aya, hakika alkur'ani mai girma yayi amfani da mafi karfin adawatul hasar shi ne (Innama ma'ana a hakika ) domin bayanin cewa mafi caccanta da al'amuran bayi shi ne Allah tabaraka wa ta'ala a tushe, bayan haka sai ma'aikinsa (s.a.w.a) sannan kuma wasu kebabbun gungu daga cikin muminai, wadannan kebabbun gungu daga cikin muminai Allah madaukakin sarki ya Ambato su da siffa kebacacciya, wannan siffa ita ce bayar da zakka ko sadaka yayin da suke cikin ruku'I, kuma wannan aya tana ishara da cewa bautarsu da Allah madaukakin sarki ba ta hanasu kiyaye hakin bayinsa da kuma biyan bukatunsu.hakika maliman tafsiri sun hadu kan cewa wannan aya hakika ta sauka ne a kan shugaban muminai Aliyu bn Abi talib (a,s) yayin da yayi sadaka da zobensa lokacin da yake cikin salla kuma yana cikin halin ruku'u ga Allah madaukakin sarki cikin masalacin Annabi (s.a.w.a), a cikin wannan aya akwai bayananiyar Magana na cewa fitaciyar siffa na tabbacin wannan kebabbun gungu shi ne shugaban muminai Aliyu bn Abi talib (a.s), kuma daga gare shi ta kasance wulayar ubangiji da Annabi Muhamadu a kan mutane, baya ga hakan wannan wulaya kuma ta kasance ga wanda yaya kama da shi (a.s) domin haka ne ma damirin ya zo ta sigar jam'I yayin da Allah tabaraka wa ta'ala ke cewa:( da kuma wadanda suka bada gaskiya, wadanda suka tsai da salla da ba da zakka a yayin da suke cikin ruku'i) a cikin wannan a kwai girman ishara na cewa wannan aya ta shafi wani da ba shugaban muminai Aliyu bn Abi talib (a.s) ba, daga cikin wadanda suka siffantu da wannan siffa, hakika kuma ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya bayyanawa al'umma da cewa hakika su ne iyalan gidansa tsarkaka da suka kasance shugabanin shiriya 12.da wannan shugabanmu Imam Sadik (a.s) cikin tafsirin wannan aya a hadisin da aka ruwaito cikin Usulul Kafi ya ce:(sai Allah  da wannan aya a kansa (ma'ana Imam Ali (a.s), sannan ya tafiyar da ni'imar 'ya'yansa da ni'imarsa, duk wanda kuma wannan ni'ima ta Shugabanci ta isar mishi daga cikin 'ya'yansa zai kasance da wannan ni'ima makamanciyar ta za su bayar da sadaka yayin da suke cikin ruku'u).

Masu saurare, abu mai mahimanci da  wannan aya ke ishara da shi , shi ne hada bautar Allah madaukakin sarki da kuma yiwa bayinsa hidima, wannan shi ne ya kebbanta ga wani gungu kebabbu daga cikin muminai da Allah madaukakin sarki ya sanya musu jibintar al'amuransa da jibintar al'amuran ma'aikinsa a kan mutane, wannan kebanta ba wai tana nufi ga wasu ahli ba a yayin da suke sadaka cikin salla yayin da suke halin ruku'u. hakika cikin tafsirin Burhan, an ruwaito wani hadisi inda a cikinsa wasu daga cikin sahabai ke cewa wallahi hakika na yi sadaka da zobe 40 yayin da nake ruku'I domin aya ta sauka a kaina kamar yadda ta sauka a kan Aliyu bn Abi talib).

*****************************Musuc*******************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, kuma kada a sha'afa shirin na karamin sani kukumi na zo muku ne kai tsaye daga sashen hausa na muryar jumhoriyar musulinci ta iran dake nan birnin Tehran,abinda ake nufi da wulayar da Allah madaukakin sarki ya sanya ga shugabanin  shiriya na iyalan gidan anabta tsarkaka cikin wannan aya, hakika na daga cikin irin wulayar Allah da ma'aikinsa a kan mutane, kuma wannan wulaya ita ce ke bayar da tabbaci na shugabanci, da kuma wajibcin yin da'a kamar yadda yake a zahiri, samuwar wani tafsiri na daban a game da ma'anar wulaya da suka babbanta , kamar taimako ko soyayya da sauransu misali shi ne abinda ita kanta ayar ta karyata ta hanyar kasancewarta ga wasu kebabbun mutane kamar yadda ayar da ta gabata tayi  bayyani kansa yayin da take bayyanin cewa yin biyayya ga Allah da ma'aikinsa da kuma wasu kebabbun gungu na muminai zai yi sanadiyar shigar mumini cikin rundunar Allah, rundunar Allah kuwa na cikin alkur'ani ana nufin muminai da imaninsu ya cika, kuma suka gaskanta wulayarsu ga Allah, da kuma kauracewarsu baki daya ga makiyansa ,wannan shi ne abinda aya ta 22 cikin suratu mujadalati tayi da shi, a fadar Allah madaukakin sarki:(Ba za ka sami mutanen da suka ba da gaskiya da Allah da ranar lahira ba suna kaunar wadanda suke gaba da Allah (ma'ana suke kangarewa) da Manzonsa, ko da kuwa sun kasance iyayensu ne ko 'ya'yansu ko 'yan uwansu ko kuma danginsu.wadancan ya rubuta (tabbatarwar Imani) a cikin zukatansu Ya kuma karfafa su da haske daga gare shi, zai kuma shigar da su aljannoni (wadanda) koramunsu suke gudana ta karkashin madawwama a cikinsu, Allah ya yarda da su, suma sun yarda da shi, wadancan ne rundunar Allah, Na'am, hakika rundunar Allah su ne marabauta) suratu mujadalati aya ta 22, wannan kuma shi ne abinda hadisai da dama suka yi tabbaci kansa, bari mu Ambato wani misali daga cikinsa, a cikin tafsirin Kanzu-daka'ik, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Babban Ja'afar Imam Muhamad Bakir(a.s) na cewa:(wani gungu na yahudawa sun karbi musulinci, daga cikinsu akwai Abdullahi ibn salam, sai suka je ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, suka ce ya ma'aikin Allah hakika Annabi Musa (a.s) yayi wasici zuwa ga Yusha'a bn Nun , wanene wasiyinka, wane ne majibncin al'amurmu bayanka? Sai wannan aya ta sauka:( Allah a hakika shi ne Mai jibintar al'amarinku da manzonsa da kuma wadanda suka bada gaskiya, wadanda suka tsai da salla da ba da zakka a yayin da suke cikin ruku'i) suratu ma'ida aya ta 55.sai ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce ku tashi mu tafi masallaci, yayin da suke isa masallaci sai ga wani mabukaci ya fito daga cikin masallacin, sai Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce ya kai wannan mabukaci shin wani bai baka wani abu ba? Sai mabukaci ya ce na'am wannan zobe, sai ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce wanene ya baka shi? Sai mabukacin ya ce wancan mutuman da yake salla, sai Ma'aiki ya tambaye shi, yana cikin wani hali ya baka zoben? Sai mabukacin ya ce yana cikin halin ruku'u. sai ma'aikin Allah (s.a.w.a) yayi kabbara, duk jama'ar da suke cikin masallacin suma suka yi kabbara, sannan Ma'aiki (s.a.w.a) ya ce: Aliyu bn Abi talib shi ne majibincin al'amuranku bayana, sai suka ce mun yarda da Allah ubangijinmu , musulinci kuma addininmu, Muhamadu kuma Annabinmu, Aliyu bn Abi talib kuma shugaba da majibincin al'amuranmu, sai Allah ya saukar da wannan aya:( Duk kuwa wanda ya sa Allah a gaba a kan al'amarinsa da manzonsa da kuma wadanda suka ba da gaskiya, to hakika rundunar Allah su ne masu rinjaye) suratu ma'ida aya ta 56.

**************************Musuc***************************

Masu saurare ganin lokaci da aka debawa shirin ya zo karshe, a nan za mu dakata, sai kuma a maku nag aba da yardarm allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimamakawa shirin har ya kamala musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da jagoranci shirin nike muku fatan alheri, wassalama alekum.