Jan 25, 2018 17:27 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,a shirye-shiryen da suka gabata mun bijuro da tambayar cewa shin ayoyin kamalar addinin da cikar ni'ima tana kafa dalili ne na khilafancin Imam Ali(a.s) shi kadai  ko kuma dukkanin shugabanin shiriya 12 na iyalan gidan anabta tsabakaka, a yau ma za mu ci gaba da bayyanin wannan maudu'I domin cikar bahasin?  kafin hakan sai a dakacemu da wannan.

************************Musuc****************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa,bayan nazari a aya ta 67 cikin suratu Ma'ida, mun fahimci cewa hakika Allah madaukakin sarki ya umarci Annabinsa mai girma na ya isarwa musulmai abinda aka saukar masa daga Ubangijinsa a cikin Hijjatu-wada'I wato hajin karshe, hakika wannan umarni na da matukar mahimanci saboda da shi ne addini yake karfafa kuma yake cika, ta yadda a bangare guda rashin isar da wannan umarni na a matsayin rashin isar da tushen sakon Ubangiji da kuma addini ba ya cika sai da shi, hakika wannan bayyani na ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya zo cikin hadisin Gadir da ya kai hadin tawaturi, inda sama da sahabai dari suka ruwaito shi a bangaren Ahlu-sunna su kadai, sannan Tabri ya wallafa littafi mai suna (Alwulaya fi dariki-Hadisil-Gadirالولاية في طريق حديث الغدير) )) inda ya tabbatar da inganci wadannan riwayoyi kamar yadda malimai da dama irinsu Suyuti, Zajri, Zahbi, Ibn Kasir da sauransu suka tabbatar da cewa hadisin mutawaturi ne.a shirin da ya gabata mun bayyana cewa hadisin Gadir na bayyani ne game da shugabanci da khilafancin shugaban muminai Aliyu bn Abi Talib (a.s) bayan ma'aikin Allah (s.a.w.a) da na shugabanin shiriya na iyalan gidansa tsarkaka 11kamar yadda hadisin sakalain yayi bayyani da kuma fadar Ma'aiki (s.a.w.a):(Duk wanda na kasance majibincin al'amuransa, Ali majibincin al'amuransa ne), hakika cikin shirin da ya gabata mun nakalto wasu hadisai da aka tabbatar da ingancinsu a bangaren ahlu-sunna, yanzu kuma za mu nakalto wani sashe na riwayar da aka ruwaito a bangaren makarantar iyalan gidan anabta tsarkaka. Cikin tafsirin Kanzul-Daka'ik a tafsirin ayar Iblaq, an ruwaito hadisi daga shugabanin shiriya Imam Bakir da Imam Sadik(a.s) , da kuma Iban Abas, jabir Ansari da sauransu daga cikin sahabai na cewa :(yayin da ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya dawo daga hajinsa ta karshe, sai mala'ika Jibrilu ya sauka da sakon Allah madaukakin sarki:( Ya kai Wannan Manzo, ka isar da abin da aka saukar gare ka daga Ubangijinka, idan kuma ba ka aikata (haka) ba, to ba ka isar da sakonsa ba, Allah kuma zai kiyaye ka daga (sharrin) mutane. Hakika Allah ba ya shiryar da mutane (wadanda suke) kafirai). Suratu Ma'ida aya ta 67,kuma wannan ya kasance a yayin da ya isa Gadir Khom, sai ya bayar da umarni a dawo da wadanda suka gabace shi, sannan kuma a jira wadanda suke baya har sai da dukkanin musulmi daga suka yi aikin hajja a wannan shekara suka tattaru wuri guda sai ma'aiki (s.a.w.a) ya jagoranci sallar Azzahar ga al'ummar musulmi a wannan wuri, bayan an kamala, sai ya tashi yayi musu Khuduba mai tsaho inda a cikin ya fada musu saukar mala'ika Jibrilu da wannan aya sannan kuma ya bayyana sababin nuzulinta, kamar yadda kuma ya karanto musu wannan aya:(Allah a hakika shi ne Mai jibintar al'amurinku da Manzonsa da kuma wadanda suka bada gaskiya, wadanda suka tsai da salla da ba da zakka, suna masu kaskantar da kai)suratu ma'ida aya ta 55 da wasu ayoyi na daban da suke bayyani kan iyalan gidan anabta tsarkaka domin su kasance a matsayin sharer fage kan isar da umarnin Allah ga Mutane na sanya wulaya da khilafanci  cikin iyalan gidansa tsarkaka, na farkonsu wasiyinsa Imam Ali (a.s) ya kuma umarci mutane da suyi masa mubaya'a, wannan shi ne abinda za mu karanto nan kadan bayan mun saurari wannan.

****************************Musuc*****************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen hausa na muryar jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, daga cikin abinda mai gaskiya amintacce (s.a.w.a) ya fada cikin Khodubar Gadir: Ya ku Mutane !wannan shi ne karshen matsayi  da zan karfafa shi a wannan wuri, ku saurara, ku yi biyayya kuma ku bi umarnin Ubangijinku, hakika Allah madaukakin sarki shi ne Ubangijinku, majibincin al'amuranku kuma bayan sa Muhamadu majibincin al'amuranku da yake khoduba a gare ku, sannan baya na Ali majibincin al'amuranku da umarnin Allah Ubangijinku sannan shugabanci ko khilafanci cikin zuriya ta daga 'ya'yana har zuwa ranar kiyama, ranar da za ku hadu da Allah da ma'aikinda,sannan tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya bayyana falalar wasiyinsa Murtadha Ali (a.s) yana mai cewa Ya Ku Mutane! Ku girmama Aliyu domin shi ne mafi falala da fifiko baya na…ta hanyarmu ce aka saukar da arziki, kuma halittu suka tsaya, kuyi nazarin Alkur'ani, ku fahimci ayoyinsa, ku yi dubi zuwa bayyanannun ayoyinsa kadda ku bi mutashabihai, na rantse da  Allah har abada babu wani da zai fassara muku shi kamar yadda yake face wanda ni, da wanda nike rike da hanunsa wato Imam Ali(a.s), ku saurara! Duk wanda na kasance majibincin al'amuransa, to Ali majibincin al'amuransa ne, kuma shi Dan uwa na, wasiyina ne, kuma wannan matsayi nasa daga Allah ne aka saukar da shi a gare ni.

Sannan tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ci gaba da bayyana sauran shugabanin shiriya na iyalansa tsarkaka, Ya Ku Mutane!Hakika Ali da tsarkakakku daga cikin 'ya'yana su ne nauyi shiiya na biyu, Alkur'ani mai girma kuma shi ne nauyin shiriya na farko, ko wane daga cikin su yana tafiya da dan'uwansa ne kuma yana gaskanta dan uwansa, har abada ba za su rabu da juna ba har sai sun tarar da ni a bakin tabki na, su ne amintattun Allah cikin halitunsa, kuma hukumominsa a doron Kasarsa, Ku saurara !hakika na sauke wannan nauyi, ku saurara! Hakika na isar, ku saurara! Hakika kuma na bayyana.

Sannan (s.a.w.a) ya ce: ku saurara!Hakika Allah madaukakin sarki ya ce, ni kuma na fada a madadinsa ku saurara, babu wani shugaban muminai face dan uwana wannan,babu wani shugabanci na muminai da ya halitta ga wani face na Ali bayana, ya Ubangiji hakika ni na shaida haka, kuma ka ishe ni shaida na isar da wannan sako, sannan ya ce Ya Ku Mutane! Hakika Allah madaukakin sarki ya cika addiniku ta hanyar bayyana shugabancinsa, duk wanda bai yi biyayya a gare shi ba da wanda ya riki wannan matsayi daga cikin 'ya'yana har zuwa ranar alkiyama, da kuma masu juwa baya ga Allah su ne wadanda suka bata ayyukansu….Ya Ku Mutane! Ku yi Imani da Allah da ma'aikinsa da hasken da aka saukar a tare da shi….Ya ku Mutane ! hasken da aka saukar daga Allah madaukakin sarki yana jikina  sannan kuma ya kwarara zuwa ga Ali, sannan kuma cikin zuriyarsa har zuwa Mahadi wanda ake jira da zai yi rigo da hakin Allah da kuma duk wani hakkinmu.,sannan ma'aiki (s.a.w.a) ya ce Ya Ku Mutane hakika na bar shugabanci ga bayana har zuwa ranar Alkiyama, kuma Hakika na isar da abinda aka umarce ni, hujja ce a kan dukkanin wadanda suka halarci wannan wuri, da kuma wadanda ba  su halarta ba, da dukkanin mutuman da aka Haifa da ma wadanda ba a Haifa ba sai nan gaba, sai wanda ya halarta ya isar ga wanda bai halarta ba, ma'aifi ya isar ga dansa har zuwa ranar Alkiyama).

Masu saurare hakika an ruwaito wannan khoduba ta anabta ranar Gadir da isnadi mabanbanta, kuma wannan da muka nakalto muku ta ishe mu tabbatar da abinda ma'aiki (s.a.w.a) ya isar da shi ranar Gadir da umarnin Ubangijinsa madaukaki da ta kumshi nassin shugabancin iyalan gidan Anabta tsarkaka har zuwa ranar tashin alkiyama. Da wannan ne kuma ya bayyana cewa kafa hujja baya yin nazari a ayoyin ikmalu-ddin da cikin Ni'ima da kuma hadisan da aka ruwaito daga bangare sunna da shi'a daga kalaman ma'aiki (s.a.w.a) dalili ne mai karfi na zabin Ubangiji ga shugabanin shiriya na iyalan gidan Anabta tsarkaka ga mutane har zuwa ranar tashin Alkiyama.

**************************Musuc***************************

Masu saurare ganin lokaci da aka debawa shirin ya zo karshe, a nan za mu dakata, sai kuma a maku na gaba da yardar allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimamakawa shirin har ya kamala musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da jagoranci shirin nike muku fatan alheri, wassalama alekum.