Sep 13, 2016 15:31 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta Yau, Ta yaya Mumuni zai tsira daga aikata shirka Ta hanyar dogaro da taimakon salla, ko azumi hakuri ko tawassuli da saurensu? Amma kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari tanadin da a aka yi mana a kan faifai.

*************************Musuc***************************

Masu saurare, Hakika a ko wata rana, cikin ko wata salla, muna karanta wannan Aya mai albarka (Ka kadai muke bauta wa, kuma kai kadai muke neman taimakonka) suratu Fatiha Aya ta 5, wannan Aya mai albarka ta bayyana mana cewa kadda mu nemi wani taimako a wajen wani face wajen Allah madaukakin sarki shi kadai, to ta yaya za mu tsira daga aikata shirka, ba za mu nemi taimako face a wajen Allah madaukakin sarki don kadda mu kaskanta? Hakika idan muka yi Nazari a cikin Alkur'ani mai girma za mu samu amsar tambayarmu, da farko tambayar da zamu fara yiwa kayuwanmu ita ce kamar yadda Aya ta 36 cikin suratu Zumar ta bayyana:(Yanzu Allah bai ishi Bawansa ba?) shakka babu hakika Allah madaukakin sarki mai iko ne ga dukkanin komai kuma shi mai tausayi ne ga Bayinsa kuma shi ya isar musu ga dukkanin abinda yake maslaha a gare su, wannan abu ne da babu wani Mumuni da zai yi kokonto a kansa. Baya ga haka, tambaya ta biyu da za ta zo mana ita ce wacce Aya ta 38 cikin wannan surat mai albarka ta Ambato (Wallahi da za ka tambaye su, wanda ya halicci sammai da kassai,Lallai za su ce:"Allah ne" Ka ce (da su):"Ku ba ni labarin wadanda kuke bauta wa Allah ba Allah ba, idan Allah ya nufe ni da wata cuta, yanzu za su iya yaye min cutar tasa, ko kuma idan ya nufe ni da rahama yanzu za su iya hana rahamarsa? Ka ce:"Allah Ya ishe ni, a gare Shi ne kawai masu dogoro suke dogara) Suratu Zumari Aya ta 38, Masu hakika babu wani Mumuni da yake kokonton cewa dukkanin abinda mutum yake dogaro ko kuma neman taimakon sa ba zai cimma abinda yake bukata ba face ta hanyar Allah madaukakin sarki.Idan kuma Allah ya nufi isar da wani Alheri ga bawansa babu wani a wannan Duniya da zai hana isar da wannan alheri ga wanda Allah ya nufa da shi.abin tambaya a nan mine ne abin fahimta cikin hakikanin akidar Alkur'ani mai tsarki? Masu saurare abinda ku da mu za mu iya fahimta cikin wannan Ayoyi na Alkur'ani shine, Neman taimako ga wanin Allah madaukakin sarki, ya kasance ko neman wani alheri ko kuma neman kariya daga wani sharri abin ki ,mai neman taimakon ba zai iya cimma gurinsa ko munufarsa ba, amma a yayin da Bawa ya nemi taimako da Allah madaukakin sarki hakika ya nemi taimako ga mai ikon komai da kuma zai kaddamar da taimakonsa  ta mafi kamalar taimako ga mai neman taimakon kuma babu wani mahluki da zai hana isar wannan taimako da Allah madaukakin ya nufa da shi.

********************Musuc**************************

Masu saurare barkanmu sa sake saduwa, ci gaba shirin zai fara da wani shahararen Hadisi wanda ke cewa (duk wanda ya nemi taimako a wajen wanin Allah ya kaskanta), Hakika Masu saurare, riko da wannan hadisi zai kasance mabudin cira daga aikata shirka ga Allah cikin babe na neman taimako, wannan Kenan, na ba biyu kuwa shine abinda zai cirar da Mumuni daga aikata shirka wajen neman taimakon wanin Allah, kaucewa meka bukatu da kuma neman taimako na komai ga wanin Allah madaukakin sarki kamar yadda Alkur'ani mai tsarki ya bayyana. Baya haka Masu saurare da dama daga cikin ku suna bayyana wannan Jumula a yayin gudanar da Salla, da iko da kuma karfinka nake tashi kuma nake ruku'I, a wannan Jumula a kwai tabbaci da kuma ikra'I na Mumuni da cewa Allah madaukakin sarki shine abin dogoro kuma a wajensa kawai ake neman taimako da bukata, bisa abinda suka bukata Masu saurare za mu fahimci ma'anar Addu'ar da aka ruwaito daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka (Ya Ubangiji kada ka barni in zamanto majibincin al'amarina ko da da kibtawar ido ne har abada) ma'anar wannan Addu'a-cikin daya daga misdakinta, shine Mutum ya yi amfani da karfin da Allah madaukakin sarki ya yi masa kuma ya yi tsamanin duk abinda yake aikatawa na shi ne, wato yayi dogaro ko neman taimako da wani abu koma bayan Allah, idan ya kasance mai neman taimako bisa wani abu ko komai na nasa koma bayan Allah zai kasance ya rasa duk wata saduwa a tsakanin da Allah madaukakin sarki da kuma duk wani taimako na gaggauwa da yake bukata domin ya sanya girman kai a zuciyar sa ya manta cewa komai yake da shi daga Allah ne domin fitar da wannan girman kai ne Ma'aikin Allah (s.a.w) ya koyar ga Al'ummar wannan Addu'a mai tarin ma'ana da ta hada dukkanin ma'anar Tauhidi.

Ya zo cikin wani sahse da wannan Addu'a da aka ruwaito cikin Littafin Misbahul-Mushtahid daga Shugabanin Shiriya iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka, inda suka bada Umarin a dinga karanta wannan Addu'a bayan ko wata salla ta Assubahi (Ya Ubangiji ga yi salati ga Annabi Muhamadu da iyalan gidansa tsarkaka kuma kada ka barni in zamanto majibincin al'amarina ko da da kibtawar ido ne har abada ko kuma ga daya daga cikin halitunka, Hakika idan ka jibinta al'amura na a gare su, ka nisantar da ni daga alheri, kuma ka kusantar da ni ga sharri, Ya Ubangiji ka sanya iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka su zamanto, shugabani na, da kuma abin koyi na, kuma ka sanya soyayyata, taimako na da kuma Addini na daga garesu kuma irin nasu, domin idan ka barni in zamanto majibincin al'amari na kaskanta), Masu saurare da wannan za mu fahimci cewa neman taimako da waliyan Allah, Mumunai, Likitoci, ko kuma kwararre a kan abinda ya kware , Neman taimako ne ga Allah madaukakin sarki idan Bawa ya sanya niyar cewa su wadannan sashe suna a matsayi wani sanadi daga Umarnin Allah tabaraka wa ta'ala, kuma Neman taimako a gare su kamar aiki da Umarnin Allah tabaraka wa ta'ala ne da ya bukaci ko wani mai bukata na ilimi ne ko magani ko kuma abinda yayi kama da hakan ya koa ga wadanda suka kware a wannan fanni, da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu iko amfani da abinda muka karanto kuma muka saurara don Albarkar Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka.

*******************************Musuc********************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.