Sep 13, 2016 15:35 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta Yau ita ce ta yaya za mu kasance masu kadaita Allah madaukakin sarki a cikin Dabi'antunmu? Kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari tanadin da aka yi mana a kan faifai.

******************Musuc***********************

Masu saurare, kamar yadda shirin ya saba, za mu fara da Littafin Allah wato Alkur'ani mai girma, A cikin Suratu Rumu Daga Aya ta 25 zuwa 26 Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Kuma tsayuwar sammai da Kassai da Umarninsa yana daga Ayoyinsa. Sannan kuma yayin da Ya kira ku kira (na tashi) sai ga ku kuna fitowa daga cikin Kasa* kuma duk abubuwan da suke cikin sammai da kassai nasa ne, dukkaninsu masu biyayya ne gare shi), A cikin suratu Nahli Aya ta 60 Allah madaukakin sarki ya ce (Wadanda  ba sa ba da gaskiya da ranar Lahira suna da mumunar siffa. Allah kuma yana da madaukakiyar siffa, kuma shi ne mabuwayi Gwani), A cikin Littafin Mu'ujamu mufradutil-Alfazil-Kur'an (معجم مفردات ألفاظ القرآن) na babban malamin nan shekh Ragib Esfahani ya ce abinda ake nufi da Wadanda  ba sa ba da gaskiya da ranar Lahira siffa ce da aka aibata Allah madaukakin sarki kuwa yana siffofi madaukaka, wato abinda ake nufi da masu wannan siffa Wadanda  ba sa ba da gaskiya da ranar Lahira , mumunar dabi'a ce da aka da aibata , Hakika daga cikin siffofinsa tabaraka wa ta'ala, kyawawen dabi'un masu girma wadanda ba sa misaltuwa kuma ba abokin misali wajen kyau da kamala. Babban malamin fikihu shekh Amuly wanda ake kira da shahidi sani wato shahidi na biyu,cikin Littafin Maskanu Fu'ad ya ce Hakika Allah tabaraka wa ta'ala ya yiwa Annabinsa Dawuda (a.s) yana yima ta'aziyar Dansa da ya rasu ya ce (Ya Dawuda ka dabi'antu da dabi'una, kuma hakika daga cikin dabi'una  a kwai Hakuri), a wani hadisin na daban kuma , an ruwaito daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(ku dabi'antu da Dabi'un Allah madaukakin sarki), Hakiaka Masu saurare  cikin wannan hadisin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya umarce mu da dabi'antuwa da Dabi'un Allah madaukakin sarki wadanda suka yi daidai da dabi'ar mutum da ta hakan ne Mutum zai cika kamalarsa ta bautar Allah madaukakin sarki hakikanin bauta, a cikin wani Hadisi za su ga  yadda Shugabanmu Imam Husain (a.s) yana tabbaka da kyakkyawar dabi'ar Allah tabaraka wa ta'ala, wajen amfani da dabi'ar Allah madaukakin sarki na rarraba arzikinsa ga dukkanin halittu, a cikin Littafin (Tuhuful Ukul) na Ibn Muhamad Hasan bn Shu'uba Alharani, an ruwaito hadisi inda a cikinsa aka ce wani Mutum a gaban Imam Husain (a.s) ya ce: Hakika kyautatawa idan ta hadu da wanda ba ahlinta zai ta rushe, sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa (abin bah aka yake ba, sai tana kasance wa mai shafar kowa kamar ruwan sama mai biyayya ga Allah zai amfani da shi kuma wanda yake sabo ma ya amfana da shi) hakika masu saurare wannan hadisi na ishara da Ayoyin Alkur'ani da dama wadanda suke bayyana fadadar arzikin ubangiji  wanda yake shafar kowa da kowa kamar fadar Allah madaukakin sarki (Dukkansu Muna wadata su ne da baiwar Ubangijinka, wadannan da kuma wadancan. Kyautar Ubangijinka kuwa ba ta zamo abar hanawa ba(wato ta hada kowa da kowa)) suratu Isra'I Aya ta 20.domin haka hakika masu saurare, wadannan Nassosi masu albarka na tabbatar mana da cewa hakika Tauhidi ko kuma kadaita Allah a dabi'unmu suna tabbatuwa da dabi'un Allah madaukakin sarki.

*******************Musuc*********************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani da mafi hadari da tabbacin shirka ko kuma yiwa Allah kishiya a bauta, shi ne dabi'antuwa da dabi'un makiyansa da fatan Allah madaukakin sarki ya tsare mu baki daya da irin wadannan munanan dabi'u. Masu saurare hakika dabi'antuwa da dabi'un Waliyan Allah ko kuma muce masoyan Allah ma'asumai iyalan gidana Ma'aikin Allah tsarkaka dabi'antuwa da dabi'un Allah madaukakin sarki ne.kuma wannan shine abinda Allah madaukakin sarki yake siffata Annabinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka da shi, misali a gurare da daman a cikin Alkur'ani mai tsarki ya siffanta shi da mai tausayi da rahama, sannan a cikin Suratu Tauba Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:( Hakika Manzo daga cikinku ya zo muku, abin da zai cuce ku yana damunsa, mai kwadayin shiriyarku, mai tausayawa kuma mai jin kayi ga mumunai) suratu tauba Aya ta 128, sannan a cikin Suratu Kalami Allah ya siffanta shi da mai dabi'u masu girma yana mai cewa (kuma Hakila kai kana kan halaye masu girma) suratu kalami Aya ta 4 sannan kuma ya yi umarni da ayi koyi da shi, sannan Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Hakika abin koyi kyakkyawa ya kasance a gare ku wajen Manzon Allah, amma ga wanda yake kaunar Allah da ranar Lahira,ya kuma ambaci Allah da yawa) suratu Ahzabi Aya ta 21 Masu kamar yadda ambaton Allah madaukakin sarki yake tabbatuwa da ambaton Ma'aikin Allah tisa da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa, haka zalika Dabi'un Allah tabarka wa ta'ala yana tabbatuwa ta hanyar koyi da Annabin Rahama Muhamadou Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka.

Takaicecciyar amsar tambayar mu ta yau, ita ce Kadaita Allah a aikaci cikin dabi'unmu yana tabbatuwa ne ta hanyar kauracewa dabi'un makiyansa da kuma dabi'antuwa da dabi'un masoyansa musaman ma koyi da dabi'un zababben Allah kuma Ma'aikin sa Muhamadou Dan Abdullahi tsira da aminicin Allah su tabbata a gare shi da kuma Dabi'un wasiyansa iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka.

***************************Musuc*************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.