Matsayin Neman taimako ga Annabi (s.a.w)
shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, a shirye shiryen da suka gabata mun yi bayyani kan ma'anar da kuma misdakin neman taimakon Allah shi kadai madaukakin sarki a dukkanin al'umura,Tambayarmu ta yau ita ce mine ne matsayin Neman taimako ga Annabin Rahama Muhamad Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da kuma na iyalan gidansa tsarkaka wajen tabbatar da neman taimakon Allah shi kadai wanda ba shi da abokin tarayya? kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari wannan.
**************************Musuc*************************
Masu saurare hakika Allah madaukakin sarki ya umarce mu da kadaita shi shi kadai a wajen bauta wajen neman taimakonsa shi kadai, Ma'ana kadda mu nemi wani taimako face wajensa madaukakin sarki, kamar yadda wannan Aya da muke karanta cikin ko wata salla tayi ishara (kai kadai muke bauta wa, kuma kai kadai muke neman taimakonka) suratu Fatiha Aya ta 5, ba shakka Addu'a na daga muhiman tabbacin neman taimako ga Allah tabaraka wa ta'ala kamar yadda shirin da ya gabata ya bayyana.to ko minene ya sanya Allah madaukakin sarki ya umarce mu da yin Addu'a ma'ana meka bukatunmu a gare shi? Idan mun koma cikin Alkur'ani mai girma cikin suratu A'arafi Aya ta 180 Allah madaukakin sarki ya ce: (Allah kuma yana da sunaye kyawawa, saboda haka ku roke shi da su, kuma ku rabu da wadanda suke fandarewa game da sunayansa, da sannu za a saka musu abin da suka kasance suna aikatawa)Hakika ya tabbata cikin bincike na tafsiri kyawawen sunayen Allah madaukakin sarki kashi biyu ne, lafziya kamar lafazin Allah madaukakin sarki ko kuma Lafazin Arrahamanu, wannan bangare shi ne wanda Aya ta 110 cikin suratu Isra'I ta yi ishara da shi, Allah madaukakin sarki ya ce:(Ka ce (da su): "ku kira Allah ko ku kira Arrahaman,kowanne kuka kira to shi yana da Sunaye ne kyawawa..) suratu Isara'I Aya ta 110.sai kuma bangare na biyu sune Sunaye takwiniya , wato mafi kamalar samuwa ma'asumai wadanda ba sa sabo kuma mafi fifikonsu wacce ke bayyani kan mafi kamalar halittun Allah madaukakin sarki su ne Annabi Muhamadou Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da kuma iyalan gidansa tsarkaka, wannan shi ne abinda hadisai da dama suka Ambato, daga cikin su Hadisin da aka ruwaito cikin Littafin Kafi na sikkatu Islam Kulaini, daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) a tafsirin Ayar da ta gabata cikin Suratu A'arafi, inda amincin Allah ya tabbata a gare shi yake cewa (wallahi mune Sunayen Allah kyawawa da Allah baya karbar wani aiki daga Bayinsa face ta saninmu), Masu saurare, ta haka za mu fahimci cewa tawassali zuwa ga Allah ta hanyar Annabi Muhamadou tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da kuma iyalan gidansa tsarkaka shine mabudin karbar Addu'a domin Aiki ne da umarnin Allah madaukakin sarki ta hanyar kiransa da kyawawen sunayansa.
A cikin Littafin Al'ikhtisas, Shekh Mufud ya ruwaito hadisi daga babban sahabin nan Jabir bn Abdullahi Al-Ansari, ya ce :na cewa Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da iyalan gidansa tsarkaka mi za ku ce dangane da Aliyu bn Abi Talib? Sai ya ce wannan Ai shi ne Ni, sannan na ce masa mi za ku ce dangane da Hasan da Husaini sai ya ce wadannan su ne ruhina kuma Fatima ma'aifiyarsu diyata ce, yana cutar da ni duk abinda zai cutar da su, kuma yana faranta min rai duk abinda zai faranta musu rai, na shaida Allah ina yaki da duk wanda yake yakarsu kuma ina zaman lafiya ko sulhu da duk wanda yake zaman lafiya ko sulhu da su, sannan sai Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce Ya Jabir idan kana so ka roki Allah ya amsa maka, to ka roke shi da sunayansu, domin su ne mafi so a wajen Allah madaukakin sarki) wannan Jumlar karshe ta Ma'aikin Allah (s.a.w) shi ne amsar tambayarmu.
***************************Musuc*******************************
Masu Saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da hadisin Shugabanmu Imam Aliyu bn Musa Arridha (a.s) wanda Allama Muhamad bn Mas'oud Al-Ayyashi ya ruwaito cikin Tafsirin sa, Imam (a.s) ya ce:( idan wani tsanani ya sauka gareku, to ku nemi taimakon Allah madaukakin sarki da mu domin Allah tabaraka wata'ala na cewa:( Allah kuma yana da sunaye kyawawa, saboda haka ku roke shi da su)suratu A'arafi Aya ta 180. Hakika hadisai da dama sun Ambato makancin wannan hadisi daga cikin su wanda aka ruwaito a bangarori guda biyu wato Sunna da Shi'a kan cewa Annabawan Allah da wasiyansu sun nemi taimakon Allah da kuma rokonsa ta hanya dogaro da Sunan Annabi Muhamadou tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka tun kafin su zo Duniya bayan da Allah ya sanar da su matsayinsu domin sune hasken Al'arshinsa, daga cikin wannan riwayoyi ya isar mana mu Ambato wacce aka ruwaito dangane da tafsirin Aya ta 37 cikin Suratu Bakara, inda Allah madaukakin sarki yake cewa (Sai Adamu ya samo kalmomi daga Ubangijinsa (wadanda ya nemi gafara da su) sai Allah ya karbi tubarsa Hakika Shi (Ubangiji) Mai yawan karbar Tuba ne, Mai yawan jin kai) suratu Bakara Aya ta 37, Hakika Suyudi cikin Tafsiru Durul-Mansur ya ruwaito hadisai da dama daga Maliman Ahlu-sunna daga Ma'aikin Allah (s.a.w) cikin tafsirin wannan Aya ya ce: (yayin da Annabi Adamu ya yi sabo, sai ya daga kansa sama sannan ya ce ina tambayarka saboda Muhamadou ka gafarta mini, sai Allah yayi wahayi a gare sa kan cewa wani Muhamadou? Sai Annabi Adamou ya ce tsarki ya tabbata a gareka a yayin da ka halicce ni na daga kaina zuwa Al'arshinka sai naga an rubuta cewa babu abin bauta sai Allah, Muhamadou Ma'aikin Allah, sai na fahimci cewa babu wani mai matsayi da girma a gareka kamar sa domin ka sanya sunansa a kusan sunanka,sai Allah madaukakin sarki ya yiwa Annabi Adamu(a.s) wahayi ya ce Ya Adamu wannan shine karshen Annabawa daga cikin Zuriyarka, kuma in ba dan shi ba, da ban halicceka ba) baya ga wannan hadisi a kwai hadisai da dama da suke ishara kan cewa Annabi Adamu (a.s) ya roki Allah madaukakin sarki da sunan Annabi Muhamadou da kuma iyalan gidansa amincin Allah ya tabbata a garesu gaba daya.
Takaicecciyar amsar tambayarmu ta Yau ita ce Nassosi da dama na hasken shiriyar Ubangiji wato Alkur'ani da hadisai sun bayyana cewa mabudin neman taimakon Allah madaukakin sarki shi ne tawasili a gare shi wato zababben zababbu Muhamadou tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da kuma iyalan gidansa tsarkaka.
*******************************Musuc********************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.