Alakar dake tsakanin Iman da Allah da na Ranar Lahira
shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta Yau, mine ne Alakar dake tsakanin Imani da Allah tabaraka wa ta'ala da kuma Imani da Ranar Lahira? Kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari wannan.
*******************Musuc*****************************
Masu Saurare Hakika Idan muka koma cikin Alkur'ani mai girma za mu ga cewa Ayoyi da dama idan suka Ambato Imani da Allah sai sun Ambato Imani da ranar Lahira, kai wasu Ayoyin ma sun bayyana cewa Imani da Allah da kuma ranar Lahira shi ne Asalin Akida da ko wani Addinin da aka saukar daga sama yayi kira a kansa, A cikin Suratu Bakara Aya ta 62 Allah tabaraka wa ta'ala y ace:(Hakika Wadanda suka ba da gaskiya (da annabawan da suka gabata) da wadanda suke Yahudawa da Annasara da Sabi'awa (duk) wanda ya ba da gaskiya da Allah da ranar Lahira ya yi kuma aiki na gari,to suna da ladansu a wurin Ubangijinsu, babu kuwa tsoro a gare su kuma sub a za su yi bakin ciki ba) abinda za mu fahimta a cikin wannan Aya mai girma shine cimma tsira zai kasance ta hanyar Imani da Allah da ranar Lahira, to ta yaya hakan zai kasance ? wannan Aya ta kanta ta bayar da amsa, bayan ambaton Imani da Allah da ranar Lahira kuma aka ce da aiki na gari, wato Imani da Ranar Lahira na daga cikin aiyukan da suka sanya Mutum aikata aiki na gari.wannan shi ne abinda Ayoyi da daman a Alkur'ani mai tsarki da kuma Hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da na iyalan gidansa tsarkaka suka yi tabbaci da shi.kamar yadda a shiri nag aba za muyi bayyani kan alamomin gaskiyar imani da Allah da ranar Lahira, amma yanzu idan muka dawo kan tambayarmu ta yau wato alakar dake tsakanin Imani da Allah da kuma ranar Alkiyama, hakika ya bayyana a cikin Aya da ta gabata cewa abune masu bin juna da ba sa rabuwa a mahangar Alkur'ani. Kuma wannan na a matsayin Asalin Imani da I'itikadi na Litattafan da Allah madaukakin sarki ya saukar kuma su ke sanya Mutum aikata aiyuka na gari da hakan zai sanya ya tsira da aikata munanan aiyuka da za su kanshi ga mumunar makoma,har ila yau Ayar da ta gabata Imani da Allah da ranar Lahira yana kare Mumuni daga duk wani tsiro da bakin ciki kuma yana kiyaye masa Ladansa,a yayin da akasin hakan kuma wato rashin Imani da Allah da ranar Alkiyama yak an jefa Mutum zuwa ga shakiyanci da kuma zalinci.A cikin Suratu Kasasi daga Aya ta 39 zuwa ta 40 Allah madaukakin sarki ya Ambato dagawa gami da girman kai na Fur'auna.inda yake cewa:(Ya kuma yi girman kai shi da rundunoninsa a bayan Kasa ba da wata Hujja ba ,suka kuma yi tsammanin cewa su ba za a komar da su zuwa gare mu ba*Sai muka kama shi tare da rundunoninsa , sannan muka watsa su a cikin kogi, to ka duba ga yadda karshen kafirai ya kasance) Hakika Masu saurare, rashin imani ga ranar Lahira shi ne musababin dukkanin matsaloli na kaucewa daga Hanya gami da Zalinci da kuma girman kai kamar yadda wannan Aya mai albarka ta bayyana.
**************************Musuc****************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, Hakika rashin Imani da ranar Kiyama na daga cikin dalilan da suke sanya mutum ya yi ta bautar Duniya yana zalintar Mutane domin shi a mahangar rayuwar ba kin Duniya kawai don haka zai ci gaba da sharholiyarsa idan yana karfi ya taka wanda yake so ya zalinci wanda yake so, har ila yau son zuciya da bin son rain a daga cikin ababen da suke sanya Dan Adam ya yi musu da ranar Alkiyama, kamar yadda Allah madaukakin sarki ke cewa:(Kuma suka ce: Ba mu da wata rayuwa sai ta Duniya, ba kuma za a tashe mu ba (ranar Alkiyama)*Da kuma za ka ga lokacin da aka tsayar da su a gaban Ubangijinsu, ya ce( da su ta harshen mala'iku) yanzyu wannan ashe ba gaskiya ba ne? su ce Lallai gaskiya ne mun rantse da Ubangijinmu. " Ya ce:To ku dandani azaba saboda abin da kuka kasance kuna kafirce (masa)*Hakika wadanda suka karyata haduwa da Allah (watau tashin kiyama) sun tabe, har sai yayin da alkiyamar ta zo musu ba zato ba tsammani za su ce:"kaitonmu kan irin sakacin da muka yi a cikkinta(watau Duniya), "suna kuwa dauke da laifukansu a bayansu. Ba shakka abin da suke dauke da shi ya munana* Rayuwar Duniya ba komai b ace illa wasa da sharholiya, kuma ba shakka gidan Lahira shi ya fi alheri ga wadanda suke jin tsoron (ta). Yanzu ba kwa hankalta ba?) suratu An'ami daga Aya ta 29 zuwa ta 32 har ila yau Masu saurare idan muka yi Nazari ga Ayoyi na 24 zuwa 26 na Suratu Jasiya za mu fahimci cewa Allah tabarka wa ta'ala ya bayyana Illar masu Jayayya saboda da son ransu kamar yadda Aya ta 23 cikin wannan Sura mai Albarka ta yi ishara da shi, watau bin son rai shine sakamakon inkari ko kuma muso da ranar Alkiyama, Allah Tabaraka wa ta'ala ya ce: (suka kuma ce "Ai ita ba wata aba b ace, face rayiwarmu ta Duniya, za mu mutu mu kuma sake eayuwa ba kuwa wani mai hallakar da mu zai zamani, alhali kuwa ba su da wani sani game da wannan, ba abin su suka yi sai zato*Idan kuma ana karanta musu ayoyinmu mabayyana(ba su da wata) hujja sai kawai suka ce: ku zo da iyayenmu idan kun kasance masu gaskiya (kan za a tashi kiyama)*Ka ce Allah ne zai raya ku sannan ya kashe ku sannan ya tara ku a ranar Alkiyama babu kokwanto a cikinta. Sai dai kuma yawaicin Mutane ba sa sanin (haka)) suratu Jasiya daga Aya ta 24 zuwa ta 26, Hakika Masu Saurare Alkur'ani mai girma a gurare daban-daban ya Ambato cewa yin muso da ranar Alkiyama ya kasance daga cikin muhuman mikami da kuma abin jayayya ga masu girman kai da Azzalimai ga Annabawan Allah masu girma amincin Allah ya tabbata a gare su, kuma da wannan ne suka jawa kansu kaucewa daga hanya, girman kai gami da Zalinci, ko da a zahiri suna kallon kansu a matsayi wadanda suka yi Imani da Allah. A bangaren guda kuma Kiran dukkanin Annabawa gaba daya sun tabbatar a kan Imani da Allah madaukakin sarki, da ranar Alkiyama da kuma Hisabi domin hakan shi zai sanya halittu su nisanta da aikata shakiyanci kuma hakan mabudi ne na kofofin tsira a gabansu.
Masu saurare takaicecciyar amsar tambayarmu na wannan shiri, shi ne a kwai alaka mai mahimanci a tsakanin Imani da Allah da kuma Imani da ranar Alkiyama wadanda su ne tushen kiran Annabawan Allah da kuma Littatafan da suka zo da su, kuma da hanyar Imani da su, tsira da kuma jin dadi gami da walwala ke tabbatuwa ga Adam.
***************************Musuc*************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.