Imani Ga Allah ya kan wajabta Imani da Ranar Lahira
shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, a shirin da ya gabata mun yi bayyani kan Alakar dake tsakanin Imani da Allah tabaraka wa ta'ala da kuma Imani da Ranar Lahira,tambayarmu ta yau ita ce shin Imani da Allah madaukakin sarki ya kan sanya imani da ranar tashin kiyama ko da ranar Lahira? Kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari wannan.
Musuc*******************************
Masu saurare kamar yadda shirin ya saba mu kan komawa kan nauyaya gudas biyu wato Alkur'ani mai girma da hadisan iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka domin neman amsar tambayarmu , da farko za mu yi nazari kan ayoyin dake bayyana mana illar samuwar ranar Lahira da kuma rayuwar ta domin sanin cewa shin za mu samu amsar da muke bukata na wannan shiri ko kuwa?A cikin suratu Kalami daga Aya ta 33 zuwa 36 Allah tabaraka wa ta'ala ya yi bayyani kan Azabar Duniya da ta Lahira ga Azzalimai kuma kyakkyawar makoma ga masu tsoron Allah, inda yace: (Kamar haka ne azaba take, kuma Hakika azabar Lahira ta fi girma da sun kasance sun san (haka)*Hakika masu tsoron Allah suna da aljannonin ni'ima a wurin Ubangijinsu* Yanzu za Mu sanya Musulmi kamar kangararru*Me ya same ku ne, yaya kuke irin wannan hukuncin?) har ila yau idan muka yi nazari cikin suratu Dukhani daga Aya ta 38 zuwa 42, za mu ga yadda Alkur'ani mai girma ya siffanta ranar Alkiyama da ranar rarrabewa, watau ranar da za a rarrabe tsakanin Mutane da sabaninsu tare kuma da yi musu hukunci, Allah tabarka wa ta'ala ya ce:(Ba Mu kuma halicci sammai da Kassai da abin da yake tsakaninsu ba don wasa ba(shiririta ba)*Ba Mu halicce su ba (sammai da kassai) sai don gaskiya, sai dai kuma yawancinsu ba su sani ba*Ranar da wani (uban gida) makusanci ba zai amfana wa makusanci (kamar aboki) komai ba, su kuma, ba za a taimake su ba* Sai wanda Allah ya ji kai, Hakika Shi, Shi ne Mabuwayi Mai Rahama) har ila yau Masu saurare, idan muka yi Nazari cikin Suratu Gafiri daga Aya ta 15 zuwa 17 ,inda Alkur'ani mai girma ya bayyana mana manufar aiko Annabawa (a.s) shi ne tsawatarwa dake a matsayin shinfida na fahimtar Ranar Alkiyama da wannan Rana ce Adalcin Ubangiji zai bayyana ga kowa, Allah Tabaraka wa ta'ala ya ce:((Ubangiji Shi) Madaukakin darajoji, ma'abocin Al'arshi, Yana saukar da wahayi daga al'amominsa bisa wanda ya so daga bayinsa don ya yi gargadin ranar haduwa (wato ranar kiyama).*Ranar da za su fuffuto (daga Kabari) babu wani abu da zai boyewa Allah a cikinsu.Shin Mulki na wannene a wannan ranar? Na Allah ne Makadaici Mai rinjaye.*A wannan ranar za a saka wa kowace rai irin abin da ta tsuwurwuta. Babu zalinci a wannan ranar, Hakika Allah Mai hanzarta hisabi ne).Masu saurare bayar karanto wadannan Ayoyi masu albarka, abinda za mu iya bayyana a matsayin dalili dake da alaka da tambayarmu shi ne Hakika wadannan Ayoyi masu albarka sun rarraba Mutane zuwa bangare biyu:musulmai da Mujrumai, wannan ita ce rayuwar Duniya, yanayin ta kuma yadda karamcin shekarun Mutane suke a cikin ta ba zai sanya ko wani Mutum ya samu cikekken sakamakon sa a cikin rayuwar Duniya, wannan ma wani dalili ne da wadannan Ayoyi masu albarka ke ishara da shi.
Musuc*******************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kamar yadda daga cikin dalilan da muka fahimta shine bayyana cikekkiyar gaskiya ba za ta bayyana a wannan rayuwa ta Duniya, idan muka yi Nazari ga rayuwar Duniya za mu fahimci cewa Salihan bayi da dama sun yi rayuwa a wannan Duniya kuma sun gushe, haka zalika da dama daga cikin Azzalimai , masu girman kai ,sarakuna da sauransu sunyi rayiwa a wannan Duniya sun gushe ba tare da sun cimma manufofinsu ba, kuma duk da irin rayuwar da aka yi a cikin ta, ba a tabbatar da cikekken adalci tsakanin Azzalimi da wanda aka zalinta a cikinta ba,kuma ba a iya warware sabanin dake tsakanin Al'umma ba, kuma ba su cimma sakamakon aiyukansu ba, na Alkheri ko na Sharri ne.dangane da wannan gaskiyar da ko wani mutum mai hankali zai iya riska, za mu fahimci cewa Imani ga Allah madaukakin sarki yak an sanya imani da Siffofinsa kyawawa, daga cikin muhimansu a kwai Adalci da Hikima, Hakika shi Allah madaukakin sarki mai hikima ne bai halacci komai don was aba, kuma shi adali ne ba zai bari a zalinci kowa a gabansa ba, kuma ba zai ki hukunta wanda aka zalinta ba kamar yadda ba zai ki yin adalci ga wanda aka zalintar ba, domin shi mai iko ne a kan komai, idan muka fahimci haka, sai ya kasance cewa Imani da Adalcin Allah madaukakin sarki da kuma hikimarsa ya kan sanya wajibcin Imani da wata rayuwa ta daban bayan wannan rayuwa wacce a cikinta za a rarrabe tsakanin mai Azzalimi da wanda aka zalinta, kuma a yi sakawa wanda aka zalintar, ita wannan rawuya wajibi ne ta kasance babu zalinci a cikin ta , kuma ba zai kasance musulmai da mujrimai su zamanto daya ba, kuma a cikin wannan rayuwa ce ko wani Dan Adam zai girbi sakamakon aikin da ya yi a wannan Duniya, idan kuma ba haka ba, to da halittar Dan Adam ta kasance wasa, kuma Allah tabarka wa ta'ala ya daukaka da yin hakan, A cikin suratu mumunun Aya ta 115 da kuma ta 116 Allah madaukakin sarki ya ce:((Allah ya ce da su) Ko kuna tsamini ne cewa Mun halicce ku ne da wasa, kuma ku ba za a dawo da Ku gare Mu ba?*To Allah sarki na gaskiya Ya daukaka , babu wani sarki sais hi, (shi ne) Ubangijin Al'arshi mai girma) Shuganmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) cikin wani hadisi da aka ruwaito cikin Littafin Ilalu Shara'I'I yayin da yake amsa tambayar wanda ya ce mine ne ya sanya Allah madaukakin sarki ya halicci halittu sai ya ce:(Hakika Allah tabaraka wa ta'ala bai halicci Halittu don was aba, kuma bai barsu kara zube hakan nan ba, ya halicce su domin bayyana kudurarsa kuma ya kallafa musu yin biyyaya a gare shi, sai su amsa da wannan domin samun yardarsa, bai halicce su kuma ba domin ya samu wani amfani daga gare su ko kuma su kare shi daga wata cutarwa, hakika ya halicce su domin ya amfane su ya kuma amfanar da su zuwa ni'ima ta har abada). Takaicecciyar amsar da za mu cimma a wannan shiri, shi ne Imani da adalcin Allah madaukakin sarki da Hikimarsa, Rahamarsa, wadatuwarsa gami da sauren siffofinsa kyawawa zai sanya Mutum ya yi Imani da wata rayuwa ta daban wato ranar Alkiyama domin a can ne Adalcin Ubangiji zai yi tajalli, da kuma rahamarsa wajen tabbatar da sakamako ga bayinsa da kuma isar da su zuwa ga Ni'ima ta har Abada.
Musuc*************************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.