Fahimtar Raunin Imani ta hanyar Nauyaya biyu
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,Tambayarmu ta yau ita ce Shin za mu iya fahimtar alamomin raunin Imani da Allah da Ranar Alkiyama ta hanyar nauyayen shiriya? Wannan tambaya na da mahimancin gaske za ta taimaka mana wajen sanin abinda ya kamata mu kaucewa abinda zai sanya Imanin gaskiya da Allah da ranar Alkiyama ya raunana .kafin shiga cikin shirin bari mu saurarin tanadin da aka yi mana a kan faifai.
*******************************Musuc************************
Masu Saurare kamar yadda shirin ya saba za mu fara da Littafin Allah madaukakin sarki inda za su fara da Aya ta karshen Suratu Mujadala a matsayin mabudin amsar tambayarmu Allah madaukakin sarki ya ce:(Ba za ka sami mutanen da suka bada gaskiya da Allah da Ranar lahira ba suna kaunar wadanda suke gaba da Allah(suke kangarewa) da Manzonsa, ko da kuwa sun kasance iyayensu ne ko 'ya'yansu ko 'yan uwansu ko kuma danginsu.wadancan ya rubuta Imani (tabbatarwar Imani) a cikin zukatansu ya kuma karfafa su da haske daga gare shi,zai kuma shigar da su aljannoni(wadanda) koramu suke gudana ta karkashinsu madawwama a cikinsu, Allah ya yarda da su,suma sun yarda da shi,Wadancan ne rundunar Allah, Na'am Hakika rundunar Allah su ne marabauta) suratu Mujadalat Aya ta 22.a kusa da wannan Aya mai girma wacce ta tattara abubuwa masu yawa dangane da wannan batu za yi Nazari a cikin wasu Ayoyi na cikin suratu Tauba wadanda suka sauko domin bayyana sifoffi na masu raunin Imani da masu karfin Imani ko kuma mu ce Imani gaskiya .Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Hakika ba mai raya masallatan Allah sai wanda ya ba da gaskiya da Allah da ranar Lahira ya kuma tsayar da salla, kuma ya ba da zakka, bai kuma ji tsoron wani ba sai Allah.To wadancan tabbas suna cikin shiryayyu*Yanzu kwa mayar da shayar da alhazai da raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya bada gaskiya da ranar Lahira ya kuma yi jihadi saboda Allah? Ai ba za su zama daya ba a wurin Allah.Allah kuma bay a shiryar da Mutane azzalumai*Wadanda suka ba da gaskiya suka yi hijra kuma suka yi Jihadi saboda Allah da dukiyoyin su da kawunansu, su suka fi daraja a wurin Allah kuma wadannan su ne marabauta) surat, Tauba daga Aya ta 18 zuwa ta 20, bayan karanto wadannan Ayoyi , tambayar da ta biyu baya itace mi ne ne za mu iya fahimta daga wadannan Ayoyi masu albarka wajen samun amsar tambayar mu ? Masu Saurare da farko abin fahimta dangane da Ayar Mujadala da ta gabata shi ne daga cikin alamomin raunin Imani da Allah da kuma ranar Alkiyama shi ne bayyana soyayya ga wanda yake adawa ko kiyayya ga Allah ko da kuwa Mutaman ya nada kusanci da kai matukar ka so shi to shakka babu imanin ka na da rauni .bayan hakan hadisai da dama sun zo domin bayyana mana misalai dangane da wannan batu, a cikin wani hadisi mai tsaho da aka ruwaito a cikin Littafin Al-Ihtijaj na Allama Tabrasi Rahamar Allah ta tabbata a gare shi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce ( Ku saurara!Hakika Makiyana su ne Ahlin Alfahasha, da Nifaki da masu ketara iyaka kuma sune 'yan uwan shaidanai wadanda suke yiwa junansu wahayi da mugayen zantuka, ku saurara! Hakika Masoyansu su ne Littafin Allah mai girma ya Ambato yana mai cewa (Ba za ka sami mutanen da suka bada gaskiya da Allah da Ranar lahira ba suna kaunar wadanda suke gaba da Allah da Manzonsa). A wani hadisi na daban Imam Sadik (a.s) ya bayyana mana wani misdaki na daban na raunin Imani da Allah da kuma ranar Lahira, shi ne gasganta masu gurbaceccen ra'ayi irin masu Gulanci,a cikin Littafin Khisal na shekh Saduk yardar Allah ta tabbatar da gare shi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:(kadan daga abinda ke gushe Imanin Mutum zama tare masu ra'ayin Gulanci watau wadanda suka fitta daga hadin Addini suna siffata Imam Ali (a.s) sama da matsayin da Allah tabaraka wa ta'ala ya kai shi, zama da su da sauraren su gami da gasganta kalaman su yana fidda imanin Mutum).
***************************Musuc**********************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani dangane da wata Aya ta cikin suratu Bara'a ko Tauba wacce za mu karanto nan gaba,wacce idan muka yi nazari za mu ga yadda ta fayyace mana alamomin raunin Imani da Allah da kuma ranar Lahira, yin Alfahari da abinda yake na zahiri ko da kuwa abinda ya shafi Addini ne ko da kuwa ya kasance shayar da Alhazai da kuma raya masallatai ne , a bangare guda kuma Ayar ta fayyace mana alamomin gaskiyar imani da Allah da kuma ranar Lahira , ta hanyar tsayar da salla,raya masallatai, da kuma Jihadi saboda Allah tare kuma da rashin jin tsaron wani face Allah madaukakin sarki. Hakan kuwa ya bayyana cikin riwayoyin da suka zo na musababi ko sanadin saukar wannan Aya mai albarka, ko da yake riwayoyin sun bayyana cewa wannan Aya mai albarka ta sauka ne har so biyu, na farko riwayar da Allama Tabrasi ya Ambato cikin tafsirinsa mai suna Majma'ul bayyan inda a ciki aka bayyana cewa Imam Ali (a.s) ya ce wa Aminsa Abas (a.s) Ya kawuna shin ba za ka yi hijra ba ka hade da ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ba? sai Abas (a.s) ya ce shin ban kasance cikin yanayin da yafi Hijra ba, Watau abinda nake yi yanzu bai fiye min yin hijra ba? ina raya Masallacin harami kuma ina shayar da Alhazan Dakin Allah? Sai wannan Aya mai albarka ta sauka domin watsi da uzirinsa) riwaya ta biyu kuwa it ace wacce take Magana a kan Shugaban mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) da aka ruwaito cikin Tafsiru Ayyashi (rahamar Allah ta tabbata a gare shi) wacce ta ke cewa:(na kasance ni da Abas da Usman bn Abi Shaiba a masallacin harami, sai Usman ya ce Ma'aikin Allah (s.a.w) ya badi makulan Ka'aba, shi kuma Abas ya ce Ma'aikin Allah (s.a.w) ya bani jagorancin shayar da Alhazai da ruwan zam-zam kai kuma ba a baka komai Ya Ali. Sai Allah tabaraka wa ta'ala ya saukar da wannan Aya(Yanzu kwa mayar da shayar da Alhazai da raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya ba gaskiya da Allah da ranar Lahira ya kuma yi jihadi saboda Allah?Ai ba za su zama daya ba a wurin Allah. Allah kuma ba ya shiryar da mutane Azzalimai) suratu Tauba Aya ta 19.
Masu saurare takaicecciyar amsar da za mu fahimta a wannan shiri, shi ne daya daga cikin alamar raunin Imani da Allah da ranar Lahira, bayyana Soyayya ko kuma biyayya ga Makiyan Allah da kuma masu fice gona da iri,na biyu kuma yin alfahari da abinda yake na zahiri har ma da abinda ya shafi addini da kuma rashin bayar da mahimanci da Asalin hakikanin Imani.da fatan Allah madaukakin sarki ya sanya mu daga cikin masu riko da hakikanin Imani don Albarkar riko da wulayar Amintatun Arrahamanu Muhamadu Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da kuma iyalan gidansa tsarkaka.
*******************************Musuc********************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.