Oct 31, 2016 03:24 UTC

shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta yau ita ce shin Imani da Allah ya kan wajabta Imani da Anbata kamar yadda Imani da Allah ke wajabta Imani da Ranar Lahira, kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari tanadin da aka yi mana a kan faifai.

**********************Musuc********************************

Masu saurare kamar yadda shirin ya saba za mu fara da Littafin Allah mai tsarki, inda a cikin suratu Ni'sa'I Allah tabaraka wa ta'ala ya amsa mana wannan tambaya a matsayin shunfuda inda yake ishara kan batun cikar hujjar ubangiji ga Bayi ta hanyar aika musu Ma'aika amincin Allah ya tabbata a gare su, Allah madaukakin sarki ya ce:(Amma masu ilimi na gaskiya daga cikin su(watau ma'abuta Littafi) da Mumunai sun ba da gaskiya da abin da aka saukar maka da kuma abin da aka saukar gabaninka, da kuma masu tsaida salla da masu bada zakka da kuma masu bada gaskiya da Allah da ranar Lahira. Wadancan ba da dadewa ba za mu basu lada mai girma (watau Aljanna)* Hakika mun yi maka wahayi kamar yadda Muka yi wahayi ga Nuhu da (sauran) annabawa da suke bayansa, Muka kuma yi wahayi ga Ibrahimu da Isma'ila da Ishaka da Yakubu da 'ya'yansa da Isa da Ayuba da Yunusa da Haruna da Sulaimanu, Muka kuma bai wa Dawuda (littafin ) Zabura* (Muka) kuma (aiko) manzanni wadanda Muka b aka Labarinsu tun tuni, da kuma wasu Manzanin da ba Mu b aka labarinsu ba. Allah kuma ya yi Magana da Musa Kai tsaye*Manzanni ne masu albishir (ga mumunai masu kuma) gargadi (ga kafirai) don haka Mutane su sami wata hujja a gun Allah bayan (aiko) manzanni. Allah kuwa ya kasance Mabuwayi ne Gwani) suratu Nisa'I daga Aya ta 162 zuwa ta 165.a gefen wadannan Ayoyi masu Albarka bari muyi Nazari dangane da Aya ta 133 da kuma ta 134 na suratu Taha, wadanda suke ishara kan rusa hujjoji Mushrika ga Annabin Rahama tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka da kuma Lutfin Allah ko tausayinsa a garesu inda ya aiko musu Ma'aikin domin cikar hujja a gare su. Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(suka kuma ce : Me ya sa bai zo man aba da wata Aya daga Ubangijinsa ba?"Yanzu bayanan da suke cikin Littattafan farko ba su zo masu ba?*In da a ce Mun hallaka su ne da azaba tun gabaninsa (wato Annabi Muhammadu), to da sun ce:Ubangijinmu, me ya sa ba ka aiko mana da wani Manzo ba sannan mu bi ayoyinka tun kafin mu wulakanta mu kuma kunyata?).suratu Daha Aya ta 133 da kuma ta 134.idan muka yi nazari za mu fahimci cewa wadannan Ayoyi masu Albarka su nada alaka mai karfi tsakanin Imani da Allah madaukakin sarki da kuma ceton halittu a ranar Lahira da kuma aiko da Ma'aika amincin Allah ya tabbata a garesu to ko wani sakamako za mu dauka dangane da hakan?Masu saurare  abin fahimta a cikin wadannan Ayoyi masu albarka shi ne hakika Allah madaukakin sarki mai iko ne a kan komai, kuma mai Hikima ne da yake sanya ko wani abu a wurin da ya dace kuma mai tausayi da yake tausayawa Bayinsa kuma ya tanadar musu dukkanmin dalilan shiriya wacce za ta ceton su daga kaskanci, bakin cikin Duniya da kuma azabar Lahira, wannan shi ne Ubangiji mai girma da ba zai yiyu ya bar bayinsa ba tare da ya aiko musu wanda zai sanar da su abubuwan da za su sanya su cimma rayuwa mai kyau madaukakiya a gidajen Duniya da Lahira kamar yadda za su tsayar da salla su kuma bada Zakka.

************************Musuc*************************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kamar yadda babu yadda za a yi Ubangiji bai bar Bayinsa hakan nan ba, ba tare da ya aiko musu mazannin da su shiryar da su ba, su yi musu galgadi na kadda su jefa kawunansau cikin musiba tare wahala da kansu ba, kuma suna kiransu zuwa ga yin tunani, musaman ma kan alkawarin da suka dauka na aikata alheri da kuma nisanatar duk wani shari, (wannan alkawari yana cikin fitirar ko wani Mutum ya dauke shi shi tun kafin ya zo Duniya) Domin haka Allah madaukakin sarki ya aiko da Ma'aika domin tunatar da mutane wannan alkwari da suka dauka domin su cika Imaninsu na fitira.wannan shi ne abinda Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) yake tunatar da mu a cikin Khudubar farko da aka ruwaito cikin Littafin Nahjul Balaga yayin da take bayyana mana ilar da ta sanya aka aiko da Ma'aika da kuma matsayin su a rayuwar Mutane, kuma wannan Khuduba tana ishaka kan Ayoyin Alkur'anin da muka nakalto cikin wannan shiri, da kuma misdakin cikar hujja ga halittu ta hanyar aiko musu da Annabawa amincin Allah ya tabbata a gare su.Imam (a.s) ya ce:(sai Allah ya aiko musu ma'aika da Annabawa domin su raya alkawarin da suka dauka na fitirarsu,su kuma tunatar da su abinda suka manta na Ni'imarsa, su cika hujjarsa ta hanyar bayyana musu hujjoji, su kuma tayar musu da karfin hankulan su dake boye, su kuma bayyana musu Ayoyin dake ishara da ikonsa gami da kudurarsa, Allah madaukakin sarki bai taba barin halitunsa ba ba tare da Annabi Ma'aiki ba ko kuma saukekken littafi ko kuma hujjar da suke bukata, ko kuma alamomin da za su shirya da su zuwa ga hanya mai haske ba..) A cikin Littafin Kafi na Sikkatu Islam Kulaini yardar Allah ta tabbata a gareshi an ruwato hadisi daga Shugaban Imam Musa Kazim (a.s) ya ce:(Hakika Allah nada Hujjoji guda biyu, hujjar da take a bayyane da kuma wacce take a boye, wacce take a bayyane it ace Ma'aika, Annabawa da Limaman iyalan gidan Annabta amincin Allah ya tabbata a gare su gaba daya, wacce kuma take boyayya shi ne Hankula da Allah madaukakin sarki ya hore wa bayinsa) watau wannan hadisi na nuni da cewa Allah madaukakin sarki yana dalilan ko hujjoji guda biyu da ya cikawa Bayin sa ya hore musu hankali da za su yi tunani su gane abinda yake na gaskiya da kuma abinda yake na karya a matsayin hujja ta badini, a matsayin hujjar Zahiri kuwa shi ne aiko da Manzanni da kuma Annabawa a matsayin wadanda suke shiryar da hankalin abinda ya kamata yayi.

Masu saurare, takaicecciyar amsar da muka fahimta a cikin nassosin da suka gabata shi ne Imani da Rahamar Allah madaukakin sarki, Hikimarsa da tausayin ga Bayi, yak an wajabta Imani da Annabta da kuma abinda aka aiko su da shi,da suke isar da shi watau sakon Allah madaukakin sarki da ke shiryar da Bayinsa zuwa ga hanyar Tsira da sa'ada a Duniya da Lahira.Dukkanin godiya, da karamci ya tabbata ga Ubangiji mai girma da  tausayi  madaukakin sarki Ubangijin Talikkai.

***************************Musuc*************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.