Nov 06, 2016 13:00 UTC

shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta yau minene manufar asali ta aiko Ma'aika ?wannan tambaya na zuwa ne bayan mun fahimci cewa Allah madaukakin sarki dan rahamarsa ga bayinsa ya aiko musu annabawa domin su shiryar da su zuwa kyakkyawar rayuwa a Duniya da Lahira, hakika masu saurare, tambayarmu ta yau wani sashe ne na tambayar da ta gabata, domin ta shafi yanayin aikin Annabawan Allah (a.s) wajen cimma rayuwa mai kyau. Amma kafin shiga cikin gadan gadan ga wannan.

******************Musuc***********************

Masu saurare kamar yadda shirin ya saba, ya kan komawa ne kan nauyaya guda biyu watau Alkur'ani mai tsarki da kuma tafarkin iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka domin samun amsar tambayar da muka bijuro da ita,da farko za mu fara da Aya ta 25 cikin suratu Hadidi, inda Ayar ke ishara da cewa tseda Adalci shi ne asasin Da'awar Annabawa Allah gaba dayansu, Allah madaukakin sarki ya ce:(Hakika Mun aiko manzanninmu da (ayoyi)mabayyana, Muka kuma saukar da Littafi da ma'auni a tare da su don Mutane tsaya da adalci  muka kuma saukar da karfe a cikinsa akwai karfi mai tsanani da kuma amfani ga Mutane, don kuwa Allah ya san wanda yake taimakonsa da Manzanninsa ba tare da sun san shi ba, Hakika Allah mai karfi ne Mabuwayi)suratu Hadidi Aya ta 25 bayan haka Masu saurare, idan muka yi nazari cikin suratu Nahali Aya ta 90 za mu fahimci cewa da farko Allah madaukakin sarki ya yi umarni da tsaida Adalci, da kuma mafi martaba ta adalci da Allah madaukakin sarki ya kira shi da kyautatawa da ya kasance mafi tsarki na kyawawen dabi'u, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Hakika Allah yana Umarni da yin Adalci da kyautatawa da kuma baiwa makusanta (taimako), Yana kuma hana barna da mugun aiki da zalunci,Yana gargadin ku don wa'anzutu) suratu Nahali Aya ta 90. Masu saurare, idan muka koma kan nauyi na biyu watau, bangaren tafarkin iyalan gidan Annabta tsarkaka, akwai Nassosi da dama da suke bayyani kan wannan Akida ta Alkur'ani mai girma, Allama Tabrasi cikin Tafsirinsa Majma'ul bayan, ya ce(an samo wata riwaya daga Usman bn Maz'un ya ce musulinta ta kasance saboda kunyar Ma'aikin Allah saboda abinda yake fada masu yawa kan Addinin musulinci, domin musulinci na bai tabbata a kan zuciyata ba,wata rana na kasance wajen Ma'aikin Allah yayin da yake nazari , sai na ga ya kalli sama kamar yana karbar sako, bayan ya dawo daga wancan yanayi sai na tambayesa kan yanayin da na gansa a ciki, sai Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce yayin da neka Magana da kai sai na ga Mala'ika Jibrilu ya zo min da wannan Aya (Hakika Mun aiko manzanninmu da (ayoyi)mabayyana, Muka kuma saukar da Littafi da ma'auni a tare da su tsaya da adalci  muka kuma saukar da karfe a cikinsa akwai karfi mai tsanani da kuma amfani ga Mutane, don kuwa Allah ya san wanda yake taimakonsa da Manzanninsa ba tare da sun san shi ba, Hakika Allah mai karfi ne Mabuwayi) Usman bn Maz'un y ace Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya karanto wannan Aya har zuwa karshen ta, sai musulinci ya samu tabbaci a zuciyata, sai na je wajen Baffansa Abu talib na bashi labarin abinda ya faru da ni lokacin da nake wajen Ma'aikin Allah (s.a.w.a) sai ya ce min Ya Zuriyar Kuraishawa ku bi Muhamadu sai ku shiryu, domin shi ba ya umartar ku da komai face kyawawen dabi'u, Usman bn Maz'un yardar Allah ta tabbata a gare shi ya ce sai na je wajen Walid bn Mugira wanda ya yi zurfi a wajen sabon Allah da shirka , na kuma karanto masa wannan Aya, sai ya ce idan ya kasance Muhamadu ne ya fadi wannan, to maddala da abinda ya fada, idan kuma ya ce Ubangijinsa to madalla da abinda ya fada) masu saurare abin fahimta a wannan hadisi shi ne Da'awa ko kuma kirar Annabawan Allah na yin Adalci, kyautatawa da kuma kyawawen dabi'u, a hakikanin gaskiya Da'awar Annabawa ta na wajbta kirar fitirar Dan Adam domin hakan ne domin haka take samun wuri da tabbatuwa a cikin zukuta.

*****************************Musuc*************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da hadisin shugabanmu Imam Sadik (a.s) da yake bayyana mana manufar da'awa ko kirar Annabawan Allah tsarkaka, a cikin Tafsirin Aliyu bn Ibrahim Kummy an bayyana cewa wani Mutum ya tambayi Imam Sadik (a.s) dangane da ma'anar wadannan Aya mai albarka(Hakika Allah yana Umarni da yin Adalci da kyautatawa) da kuma wannan Aya (ya yi umarni cewa kada ku bauta wa kowa sai Shi kadai) sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa Na'am babu wani abu da Allah madaukakin sarki zai umarci bayinsa face akwai adalci da kyautatawa,kuma Addu'ar Allah ta shafi kowa da kowa, ita kuma shiriya ta wani sashe ne, kamar fadar sa (yana shiryar ga wanda yake so zuwa hanya madaidaiciya, bai ce ba kuma yana shiryar da dukkanin wadanda suka roke shi zuwa ga hanya madaidaiciya) abin fahimta a wannan hadisi shi ne Adalci da kyautatawa ba sa samun tabbatuwa sai da bautar Allah madaukakin sarki, kuma wannan shi ne wata fuska ta daban daga cikin manufar sakwanin Annabawan Allah tsarkaka, idan kuma Bawa ya zamanto mai gaskiya a du'a'insa da kuma fuskanta zuwa ga Ubangiji, manufar sakon Annabta zai tabbatu a cikin zuciyarsa kuma zai cimma rayuwarsa cikin adalci da kyautatawa.A cikin Littafin Khisal na Shekh Saduk an ruwaito wani hadisi inda a cikin sa aka ce wani Mutum ya tambayi Imam Zainul Abidin (a.s) ya ce Ya Dan Ma'aikin Allah ba ni labarin dukkanin hukunce-hukuncen Addini, sai Imam (a.s) ya amsa da cewa (fadar gaskiya, hukunci da adalci, cika alkawari da Adalci) wadannan su ne dukkanin hukunce-hukuncen Addini) har ila yau a cikin Littafin na Khisal, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce :a cikin Littafin Imam Ali (a.s)   ya ce halaye uku mai yin su ba zai mutu ba har sai ya hadu da kaicon su, Zlinci, yanke zumunci, da kuma shaidar karya).

Masu saurare, takaicecciyar amsar da za mu fahimta daga wadannan Nassosi masu albarka dangane da shirinmu na yau, shi ne hakika hadafi ko kuma mnufar dukkanin sakonin Annabawan Allah tsarkaka shi ne sanya Mutane su yi rayuwa bisa tushan Adalci da insafi, kyautatawa da kuma kyawawen dabi'u, kuma hakan na samuwa ne ta hanyar bautar Allah da bin umarnisa, kuma wannan shi ke tabbatar musu da tsarkakkekiyar rayuwa mai kyau a Duniya da Lahira.da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu taufiki da wannan dabi'a, dan albarkar riko da wulayar Annabi Muhamadu da kuma iyalan gidan sa tsarkaka amincin Allah ya tabbata a gare su baki daya.

***************************Musuc*************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.